A ranar 12 ga watan Agusta ne dai aka gudanar da ranar matasa ta duniya.
Batun ko wa za a iya kira matashi dai ya sha ban-ban tsakanin kasashen duniya.
Majalisar dinkin ta sanya wanda za’a iya kira matashi shine daga dan shekara 15 zuwa 24.
Itama hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta bayyana wanda za’a iya kira matashi shine wanda yake tsakanin shekaru 15 zuwa 24.
To amma Asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce matashi shine dan shekaru 14 zuwa 29.
A Turai kuma matashi shine dan shekaru 14 zuwa 24 to amma kuma matasa sune ‘yan shekaru 14 zuwa 29 a wasu lokutan kuma yana kai har yan shekaru 35.
Idan muka dawo Najeriya kuma a hukumance matashi shine dan shekaru 15 zuwa 29 bayan da gwamnatin kasar ta sauya daga tsohon tsari a shekarar 2019 wanda a baya Najeriya na ganin matashi shine dan shekaru 18 zuwa 35.
Kasashen Afrika da dama dai na daukar matashi shine dan shekaru 18 zuwa 35.
A yanzu haka duk wanda yayin kammala jami’a ya kasance ya haura shekaru 30 bazai yi hidimar kasa ba wato NYSC. Wannan na cikin abinda ke nuna ko waye matashi a hukumance a Najeriya.
To duk da wannan sauyi a Najeriya kungiyoyin matasa na NYCN, majalisar dokokin matasa wato Youth parliament da sauransu masu jagorancin sun haura shekaru 30 wasu ma sun kai kusan 40.
