Fayyace abubuwaWaɗanne ƙasashe ake ganin suna goyon bayan kafa gwamnatin...

Waɗanne ƙasashe ake ganin suna goyon bayan kafa gwamnatin ƴan tawaye a Sudan?

-

Ayyana gwamnatin ƴan tawaye da jagoran RSF Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya yi a Sudan, ya zo a daidai lokacin da yaƙin basasar ƙasar ke cika shekara biyu, wanda ke nuna cewa yanzu kasar ta rabu gida biyu.

Ƙasashe da ake ganin suna goyon baya da kuma tattaunawa da gwamnatin ƴan adawa ta RSF sun hada da, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE da Kenya da Chadi da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Habasha da kuma Uganda. Akwai kuma wani ɓangare na Sojojin Libya da suka ɓalle.

A lokacin da yake ayyana kafa gwamnatin adawa a ranar 15 ga watan Afrilu wannan shekarar, Laftanar-Janar Mohamed Hamdan Dagalo ya godewa Habasha da Chadi da Uganda da kuma Kenya. Birnin Nyala na yankin Darfur ne zai zama  fadar gwamnatin ta RSF da kungiyoyin kawance. Yawancin ƙungiyoyi da ke riƙe da makamai da kuma na siyasa sun yi yarjejeniya da RSF a watan Fabrairun bana, kan kafa gwamnatin da za ta fito daga yankunan Darfur da Kurdufan.

A watan Fabrairu, Al-Hadi Idris Yahya, babban jigon ƙungiyar Tasses ya yi iƙirarin cewa “suna da yakinin za su samu goyon baya daga ƙasashe da dama” kan kafa gwamnatin.

Ayyana gwamnatin ya ƙara janyo rarrabuwar kawuna a Sudan da kuma saka fargabar cewa ƙasar za ta faɗa cikin mawuyacin hali la’akari da halin gwamnatoci biyu da ake dasu a Libya.

RSF da ƙawancen ƙungiyoyi sun bayyana shirin fito da “sabuwar takardar kuɗi da kuma takardun zama ɗan ƙasa”, wanda masana ke ganin yunkurin ɓallewa ne.

Sai dai, Dagalo ya yi watsi da zargin neman ɓallewa daga Sudan. A maimakon haka, ya zargi gwamnatin sojin ƙasar da yin wasu abubuwa da za su kai ga rabewa, da kuma dawo da irin kuskuren da ya janyo ballewar Sudan ta Kudu.

Gwamnatin ƴan adawar za ta samar da sojoji da kuma ƴan sanda iri ɗaya, yayin da RSF da ƙungiyoyin ƙawance na ƴan bindiga za su kasance jigon dakarun.

Majalisar Ɗinkin Duniya, Ƙungiyar Tarayyar Afrika AU, Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Tarayyar Turai EU da kuma Amurka sun nuna adawa  da batun kafa gwamnatin ƴan tawaye da kuma nuna goyon baya ga haɗin-kan Sudan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Shin da gaske akwai ‘yar tsama tsakanin Tinubu da Kashim?

Tun bayan dawowar damakradiyya a shekarar 1999 za’a iya cewa samun rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa ba...

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Karanta wannan

Shin da gaske akwai ‘yar tsama tsakanin Tinubu da Kashim?

Tun bayan dawowar damakradiyya a shekarar 1999 za’a iya...

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar