Tun lokacin matsalar cutar Covid-19 jami’o’i a fadin Najeriya suka fara karfafa karatu ta yanar gizo wato online. Duk da cewa akwai jami’ar NOUN da ta dade tana gudanar da karatu ta yanar gizo ga dalibanta. Hakan bai hana sauran jami’o’i suma samar tare da karfafa wannan bangare ba.
Batu:
Akwai wani sako dake yawo a shafin Facebook wanda ke nuna cewa jami’ar Abuja tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi na samar da kwasa-kwasai ta yanar gizo kyauta ga al’ummar kasar.
Wani shafin Facebook mai suna Lifeserviced ya wallafa wannan sanarwa (archived here) kamar haka:
“Darussan Fasaha na Kan layi Kyauta
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da hadin gwiwar Jami’ar Abuja na samar da kwasa-kwasan kan layi kyauta ga al’umma a fadin kasar nan 18-30 shekaru 31-50 shekaru 51-70 shekaru”
Mutane da dama dai sun tofa albarkacin bakin su a wannan wallafa inda suke neman yadda zasuyi rijista. Yayin da wasu da dama suke yada wato shares.

An sami irin wannan wallafa da take cewa jami’ar Najeriya dake Nsukka itama tana samar da kwasa-kwasai kyauta ta yanar gizo.

Bincike:
Alkalanci ya binciki wannan wallafa wanda da farko dai Hausar da akai amfani da ita ba mai kyau bace domin an fassara “online” a matsayin “kan layi” sannan kuma anyi amfani da hoton tsohon shugaban jami’ar Farfesa Abdulrasheed Na’Allah mai makon Shugabar riko ta jami’ar wato Farfesa Aisha Maikudi.
Sannan Alkalanci ya tuntubi mai magana da yawun jami’ar Abuja din Dr. Habib Yakoob inda yace “Sanarwar karya ce, kuma jami’ar Abuja bata yin wani kwas na yanar gizo kyauta.”
Sakamakon Bincike:
Binciken Alkalanci ya gano cewa wannan sanarwa karyace da kuma kokarin zambatar mutane da wasu ke kokarin yi.