Gwamnan jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya ya bayar da umarnin rufe tare kwace lasisin gidan radiyo mai suna Badeggi FM, saboda zargin Ingiza mutane su tada tarzoma wanda gidan radiyon ya musanta.
Wa zai iya rufe gidan radiyo?
Kundin tsarin mulkin Najeriya sashe na 39 ya baiwa ‘yan kasa damar mallaka tare da bude gidan jarida…
Dokar Najeriya dai ta baiwa hukumar kula da kafafen yada labarai NBC damar cin tara, soke lasisi tare da rufe kafar yada labarai Idan har an sami kafar da laifi bayan bincike.
Shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya Afam Osigwe ya ce “babu wanda doka ta bashi damar rufe gidan jarida ba tare da bin doka ba.”
Itama ma’aikatar yada labarai ta Najeriya a wata sanarwar manema labarai da mai baiwa ministan yada labarai shawar Rabi’u Ibrahim ya sanyawa hannu ta tabbatar da cewa hurumin rufe ko soke lasisin gidan jarida na karkashin hukumar kula da kafafen yada labarai ta Najeriya wato NBC ce kawai.
Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatin jihar ta Neja da ta mika korafinta kan gidan jaridar ga hukumar NBC.
Sakamakon bincike:
Bisa bayanin kundun tsarin mulkin Najeriya, kungiyar lauyoyi ta kasa da kuma ma’aikatar yada labarai ta Najeriya suka tabbatar da cewa hurumin dakatar ko soke lasisin gidan jarida na hannun hukumar NBC ne ba wata hukuma ko gwamnatin jiha ba.
