Wutar California dai ta haddasa da kuma cigaban samun labaran karya da dama a tsakanin mutane da dama a shafukan sada zumunta.
Batu:
A ranar 12/01/2025 wani mai suna Mubarak Garba Yabo ya wallafa wani ikirari (archived here) da hoto a shafin kafar sada zu na Facebook inda ya rubuta; “A ƙarshedai ita ma abar bautar da kanta ta sha wuta , balle ta kare masu bautar ta…”
Hoton dake kasan wancan ikirari dai shine Statue of Liberty na kasar Amurka.

Bincike:
Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta fara da binciken me gunkin Statue of Liberty yake nufi a kasar ta Amurka.
A cewar shafin hukumar gandun daji da adana kayan tarihin Amurka shi gunkin Statue of Liberty kyauta ce da mutanen kasar Faransa suka baiwa Amurka a matsayin alamar ‘yanci da kuma damokradiyya.
An kaddamar da Statue of Liberty a watan Okotban shekarar 1886. Sannan an sanya shi a matsayin abun tarihi na kasa a shekarar 1924.
Shafin Britannica tace tsayin wannan gunki ya kai tsawon kafa 305 wato kwatankwacin mita 93.
Kuma yana nan ne a birnin New York na Amurka.
Masanin tarihin kasar Faransa mai suna Edward de Laboulaye bada shawarar kyautar ta Statue of Liberty ga Amurka, wanda mutanen kasar ta Faransa suka yi karo-karon kudi.
Sannan Kasancewar wanna statue yana birnin New York ba jihar California da aka sami wutar daji ba, kafar Alkalanci bata sami wani sahihin labarin cewa Statue of Liberty ya ci wuta ba.
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanai kan tarihin wannan Statue of Liberty na kasar ta Amurka da kuma dalilin yinsa. Sannan babu inda aka bayyana shi a matsayin abin bauta, face gurin tarihi da masu yawon bude ido suke zuwa. Sannan babu wani labari dake nuna Statue of Liberty ya kama da wuta. Hakan ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa wancan iƙirari ƙarya ne.