BindiddigiShin an nemi wulakanta Shugaban Burkina Faso a Faransa?

Shin an nemi wulakanta Shugaban Burkina Faso a Faransa?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa tabbatar da cewa shugaban na Burkina Faso bai taba kai ziyara Faransa ba tun bayan juyin mulkin da yayi. Kuma babu wani bayani daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Burkina Faso daya nuna cewa yaje Faransa, da kuma tabbatar da cewa bidiyon da ake yadawa an samar dashi ne ta amfani da kirkirarriyar basira AI. Hakan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin karya ne.
A cikin ‘yan shekarun nan an cigaba da samun labaran karya musamman dake da alaka da kasar Burkina Faso.
Ikirari:
Wani shafin Facebook mai suna Rahama TV ya wallafa wani labari ranar 23/04/2024 dake ikirarin cewa an nemi a wulakanta shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Traore a filin tashi da saukar jiragen kasar Faransa dake Paris. Kadan daga cikin abinda aka ce a labarin;
“… A rashin sani wasu ma’aikatan filin jirgin daman suka nemi su wulakanta shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Treore. Shugaban ta Burkina Faso yaje Faransa ne shi kadai zikai ko dan sanda babu. Ballantana soja, ko masu daukar hoto wato ‘yan jarida, haka ya tafi filin jirgin na Paris domin komawa kasar ta Burkina Faso. Can kuma anyi dandazo ana ta jiransa…”
Wannan wallafa ta sami shares sama da dari takwas, comments sama da dari biyu da hamsin. Sannan mutane sama da dubu arba’in ne suka kalla.
             Hoton labarin karya dake cigaba da yaduwa
Haka zalika bisa lura da hoton dake rahoton ya nuna cewa an dakko labarin ne daga wasu kafafen sada zumunta da suke ta yada bidiyon da kuma yin wadannan ikirari a karshen turancin Ingilishi.
Bincike:
Kafar tantance labarai, bin diddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa bidiyon da akai amfani dashi wajen hada wannan rahoto, bidiyo ne da akai amfani da kirkirarriyar basirar AI, wato dai shi kansa bidiyon hadashi akayi ba na gaskiya bane.
Haka zalika babu wata kafar jarida data taba rawaito cewa shugaban na Burkina Faso ya taba kai ziyara kasar Faransa tun bayan juyin mulkin da yayi.
Babu wannan labari kuma a shafin ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso bayan da Alkalanci ta bincika.
Sannan babu wani labari ko rubuta daga hukumomin kasar ta Burkina Faso da Faransa da ke nuna cewa ya taba zuwa kasar Faransa tun bayan juyin mulkin da yayi.
Tun bayan zaman Ibrahim Traore shugaban kasar Burkina Faso alaka tsakanin kasar da Faransa tayi tsami.
Har ila yau labarin ya yi ikirarin cewa baturiyar da aka gani a bidiyon ta bukaci taga boarding pass din shugaban kasar saboda wai bai sanya kaya mai tsada ba, kuma babu agogo a hannunsa.
To sai dai a bidiyon da aka nuna shugaban na Burkina Faso na sanye da wando da kuma hular soja.
Kuma ma’aikatan cikin jirgin basa tambayar boarding pass a cikin jirgi Idan ba dalili na su nunawa mutum gurin zaman sa ba ne.
Sakamakon bincike:
Bisa rashin samun labari ko bayani daga wata kafar yada labarai sahihiya da ta taba rawaito cewa shugaba Traoré ya taba kai ziyara Paris tun bayan juyin mulki. Da kuma binciken da ya tabbatar da cewa bidiyon ba na gaskiya bane wato an samar da shi ne ta kirkirarriyar basirar AI. Haka zalika bayanan cikin labarin masu cin karo da juna ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar