Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun zaman majalisar dattawa da Sanata Sani Musa yayi maganar dake bidiyon da ake yadawa shekara daya da ta wuce, wanda baida alaka da batun komawa nakaranta koyon turanci ko kuma hirar da Kawu Sumaila yayi da gidan talabajin na Channels. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa Kawu Sumaila ya koma makarantar koyon turanci karya ne.
Ikirari:
Wani shafin Facebook mai suna Premier Radio 102.7 FM ya wallafa labarin cewa wani Sanata mai suna Sani Musa ya gabatar da koke ga Majalisar dattawa kan yadda Sanata Kawu Sumaila yayi turanci a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV.
Wani shafin na Facebook mai suna Hausa News Reports shima ya wallafa wannan ikirari.
“ Wani ɗan majalisa yayi kira ga kawu Sumaila kan cewa ya koma Makaranta ya koyi Turanci, inda ya bayyana cewa Yakamata Ace kawu Sumaila yana Makarantar koyan turanci”
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta bi diddigin bidiyon da ake yadawa inda ta gano cewa Sanata Sani Musa yayi magana ne a ranar 12 ga watan Maris, shekarar 2024, ranar da majalisar dattawa ta dakatar da Sanatan Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi.
Haka zalika bayan sauraron maganganun Sanata Sani Musa ya nuna cewa kalaman turancin da basu kai darajar majalisar dattawa ba musamman sakon WhatsApp da Kawu Sumaila ya tura zuwa group din Sanatocin arewa.

Sakamakon Bincike: