BindiddigiSanata Sani Musa bai ce Sanata Kawu Sumaila ya...

Sanata Sani Musa bai ce Sanata Kawu Sumaila ya koma makarantar koyon turanci ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun zaman majalisar dattawa da Sanata Sani Musa yayi maganar dake bidiyon da ake yadawa shekara daya da ta wuce, wanda baida alaka da batun komawa nakaranta koyon turanci ko kuma hirar da Kawu Sumaila yayi da gidan talabajin na Channels. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa Kawu Sumaila ya koma makarantar koyon turanci karya ne.

 

Ikirari:
Wani shafin Facebook mai suna Premier Radio 102.7 FM ya wallafa labarin cewa wani Sanata mai suna Sani Musa ya gabatar da koke ga Majalisar dattawa kan yadda Sanata Kawu Sumaila yayi turanci a wata hira da gidan Talabijin na Channels TV.
Wani shafin na Facebook mai suna Hausa News Reports shima ya wallafa wannan ikirari.
Wani ɗan majalisa yayi kira ga kawu Sumaila kan cewa ya koma Makaranta ya koyi Turanci, inda ya bayyana cewa Yakamata Ace kawu Sumaila yana Makarantar koyan turanci
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta bi diddigin bidiyon da ake yadawa inda ta gano cewa Sanata Sani Musa yayi magana ne a ranar 12 ga watan Maris, shekarar 2024, ranar da majalisar dattawa ta dakatar da Sanatan Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi.
Haka zalika bayan sauraron maganganun Sanata Sani Musa ya nuna cewa kalaman turancin da basu kai darajar majalisar dattawa ba musamman sakon WhatsApp da Kawu Sumaila ya tura zuwa group din Sanatocin arewa.
Hoton bidiyon da ake yadawa
Sakamakon Bincike:
Bisa samun zaman majalisar dattawa da Sanata Sani Musa yayi maganar dake bidiyon da ake yadawa shekara daya da ta wuce, wanda baida alaka da batun komawa nakaranta  koyon turanci ko kuma hirar da Kawu Sumaila yayi da gidan talabajin na Channels. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin cewa Kawu Sumaila ya koma makarantar koyon turanci karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar