BindiddigiMenene Hadin Kungiyar Lakurawa Da Harin Kebbi?

Menene Hadin Kungiyar Lakurawa Da Harin Kebbi?

-

Shalkwatar tsaro ta Najeriya dai ta tabbatar da wanzuwar wata kungiya data kira ta “yan ta’adda” mai suna Lakurawa dake da sansani a jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya.
Su dai wadannan Lakurawa anyi ittifakin cewa sun fito ne daga kasashen dake da makwabtaka ta kusa ko ta nesa da Najeriya wato irin su Chadi, Nijar, Mali, Burkina Faso da sauran su.

Batu:

Akwai labaran dake yaduwa cewa kungiyar ta lakurawa takai hari a garin Mera na jihar Kebbi kuma sun kashe mutane da dama. Misali; Sabuwar kungiyar ‘yan bindiga da ake kira da Lakurawa ta hallaka mutane 15 tare da kore shanun makiyaya sama da 100 a jihar Kebbi.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Alkalanci a bincikenmu mun fara da nemo shin kungiyar ko muce mutanen sababbin shigowa Najeriya ne? A inda muka sami tabbacin cewa wadannan mutane da ake kira Lakurawa sun dan jima a yankunan Gwadabawa, Tangaza, Illela, Binji a inda suke zaune a dazukan wadannan wurare.
Mun tuntubi Detective Bala Yakasai mai sharhi tare da bincike kan harkokin tsaro yace; “Dangane da Lakurawa da suka bullo a jihar Sokoto da Kebbi gaskiya ne domin kuwa sun haura akalla watanni uku da zama a wannan yanki, wadannan Lakurawa suna yare na Fulatanci, Buzanci da wasu yaruka. Akwai kyakkyawan yakini na cewa akwai babbar kungiyar ta’addanci dake goya musu baya da daukar nauyin su.”
Akwai wani kaulin dake ikirarin cewa mutanen wannan yanki ne suka bukaci Lakurawa suzo dazukan domin karesu daga harin yan fashin daji wato bandits.
Haka zalika binciken ya kara tabbatar da cewa Lakurawa nada akida data sha banban data mutane dake zaune a wadannan yankuna domin suna gudanar da harkokin addini da za’a iya cewa yana kaman ceceniya da akidar kawarij koma Boko Haram domin suna barranta kansu daga gwamnati, shugabancin damakradiyya, dama sarakunan gargajiya.
Suna amfani da kudi dama shanu wajen jan hankalin matasa da mata shiga wannan kungiya.
Sannan an tabbatarwa Alkalanci cewa ba’a ga miciji tsakanin Lakurawa da yan fashin Daji wato bandits.
Detective Yakasai yace; “Babu abinda ya hada Lakurawa da bandit na kusa Ko na nesa in banda yaren Fulatanci, domin su Lakurawa na fakewa da addini ne a inda bandits kuma neman kudi ne.”

Lakurawa A Jihar Kebbi?

Alkalanci mun tuntubi mazauna jihar Kebbi musamman yankunan dake da iyaka da jihar Sokoto dama jami’an tsaro a yankin arewa maso yamma inda aka tabbatar mana da cewa ya zuwa yanzu dai babu yan kungiyar ta Lakurawa a jihar Kebbi.
Wani jami’in tsaro yace; “Saboda rahoton shalkwatar tsaro da aka fitar yan kwanaki kadan kan Lakurawa shine zaisa yanzu duk wani hari a wannan yankin mutane na iya zargin Lakurawa, duk da cewa babu tabbacin hakan domin duk da suna da makamai basu fara sata Ko kai hari kan mutane ba, face ma sune suke baiwa mutane kudi don su shiga kungiyar.
Sannan mun tuntubi mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar ta Kebbi Yahaya Dan Jada inda ya tabbatar da cewa a hukuman ce gwamnatin jihar bata sami rahoton cewa akwai Lakurawa a jihar ba sai dai dama jihar na fama da hare-haren ‘yan fashin daji wato bandits.

Abinda Ya Faru A Harin Kebbi!

Idan muka dawo batun harin na garin Mera a jihar Kebbi inda aka kashe mutane goma sha biyar Alkalanci ya kara bincikawa kan Lakurawa ne ko suwaye?
Mazaunin garin na Mera da abin ya faru a gaba idonsa yace “A ranar Juma’a da abin ya faru dai yawancin mutane na masallacin Juma’a sai akayi yekuwar cewa yan fashin daji sun kwace shanu sun kada su suna tafiya, daga nan ne sai mutanen dake da shanu da kuma yan banga suka dauki makamai domin zuwa kwato dukiyarsu wanda daga nan ne aka kashe wasu da dama. Suma yan fashin dajin an kashe wasu.”
Alkalanci mun tuntubi wani daga cikin yan banga wanda yana cikin wadanda suka fafata da wadannan mutane kuma yasha da kyar inda yace “Ina mai tabbatar maka cewa yan fashin daji ne, domin na sami nasarar kashe daya daga cikin su.”
Da muka tambayeshi kan labarin da ake cewa Lakurawa ne, sai yace; “Ni dai bana tunanin Lakurawa ne, domin kuwa na gansu da idona, ai ba’a wuce shekara daya bama yan fashin da jin sunyi kokarin kawo hari wannan gari basu sami nasara ba.”
Har ila yau mai sharhin tsaro Zagazola Makama yaceLakurawa basu taba kai hari a kan fararen hula a jihar Kebbi ba, wannan hari da aka kai yan fashin daji ne.”
Har ila yau mai sharhin tsaro Zagazola Makama yace “Lakurawa basu taba kai hari a kan fararen hula a jihar Kebbi ba, wannan hari da aka kai yan fashin daji ne.”
Har ila yau mai sharhin tsaro Zagazola Makama yace “Lakurawa basu taba kai hari a kan fararen hula a jihar Kebbi ba, wannan hari da aka kai yan fashin daji ne.”
To amma Detective Yakasai na ganin cewa da Lakurawa aka fafata. “ su Lakurawa basu zo kai tsaye su fara kai hari tun wannan lokaci ba, wannan ma daya faru sun sami takaddama ne da matasan jihar ta Kebbi ya kai an fara harbe-harbe wanda yayi silar mutuwar da yawa harda su Lakurawa, sun sami nasarar kwashe nasu da aka kashe Ko akajiwa rauni.”
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya data dauki nauyin harin na jihar Kebbi.
Shekaru da dama dai jihohin arewa maso yammacin Najeriya dai na fama da matsalar yan fashin daji dake satar shanu, mutane wasu lokuta kuma kashe mutane da kona kaiyuka.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar