Hukunci: Ƙarya ne
Dr. Bello Galadanchi wanda aka fi sani da Dan Bello ya tabbatarwa kafar tantance labarai ta Alkalanci cewa, matar sa Aisha Maikano na raye, kuma ta cigaba da wallafa bidiyo wanda ta saba a shafin ta na Facebook. Wannan yasa Alkalanci yanke hukunci cewa bidiyon da wani shafin Tiktok ke yadawa cewa matar Dan Bello ta rasu karya ne.
Ikirari:
Wani shafin TikTok mai suna @danbello307 ya wallafa wasu faifan bidiyo tare da ikirarin cewa matar Dr. Bello Galadanchi wanda aka fi sani da Dan Bello ta rasu.

Bincike:
Kafar tantance labarai, bin diddigi da bincike ta Alkalanci ta fara duba sahihan shafukan na Dan Bello a TikTok, Facebook da X (Twitter) babu wannan labari. Haka zalika mun tuntubi Dan Bello kai tsaye inda ya turawa Alkalanci bidiyon da matar ta shi Aisha Maikano ta wallafa a shafin ta na Facebook.
Wanda ya tabbatar tana raye.
Sakamakon bincike:
Bisa tabbatar da cewa matar Dr. Bello Galadanchi wanda aka fi sani da Bello Galadanchi na raye, da kuma yadda ta cigaba da fitar da bidiyo a shafinta na Facebook ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyon da ke cewa matar Dan Bello ta rasu karya ne.
