Lafiyar kwakwalwa wato mental health lalura ce da ake kace-nace a kanta tare da kokarin ganin an wayar da kan mutane to sai dai akwai wasu tatsuniyoyi da shaci fadi wato myth masu yawa dangane da wannan batu.
Na daya
Idan mutum ya sami matsalar lalurar lafiyar kwakwalwa, hakan na nufin baida basira ne.
Bincike:
Lalurar lafiyar kwakwalwa itama kamar sauran lalurori da ake iya gani Ko ji ne, domin tana iya samun kowanne irin mutum mai basira ko dakiki, mai kudi ko talaka, mai ilimi ko jahili.
Sakamakon Bincike:
Wannan ikirari ba gaskiya bane
Na biyu
Yara basa samun matsalar lalurar lafiyar kwakwalwa suna samun fushi ko farin ciki dalilin sauye-sauye na halitta wato hormones.
Bincike:
Tabbas yara tsakanin shekaru goma zuwa sha biyar na samun daukewar farin ciki da dawowar sa, to amma hakan ba yana nuna cewa basa samun lalurar lafiyar kwakwalwa ba. Kashi 50 na lalurar kwakwalwa na farawa ne daga shekaru 14 a cewar asusun kula da yara na majalisar dinkin duniya haka zalika kashi 20 na yara na fama da wannan lalura, haka zalika lalurar na daya daga cikin abinda ke haddasa yara yan shekaru 10 Zuwa 15, 15 zuwa 19 kashe kansu a fadin duniya.
Sakamakon Bincike:
Wannan ikirari ba gaskiya bane
Na uku:
Zaka kula da lafiyar kwakwalwa ne Idan kana da matsalar lalurar lafiyar kwakwalwa.
Bincike:
Kowa zaici riba Ko gajiyar lafiyar kwakwalwa Idan ya kula Ko ya dauki matakin tabbatar da lafiyar kwakwalwar sa. Shi yasa a harkar lafiya ake cewa rigakafi yafi magani.
Sakamakon Bincike:
Wannan ikirari ba gaskiya bane
Na hudu
Mutanen dake da abokai da yawa suna haba-haba da mutane bazasu sami lalurar lafiyar kwakwalwa ba damu babu abinda zai sanya musu damuwa.
Bincike:
Lalurar matsananciyar damuwa wato depression na cikin lalurar lafiyar kwakwalwa, wanda abubuwa da yawa ke haddasa wa. Kowanne irin mutum na iya kamuwa da Lalurar damuwa wato depression.
Misali yaran dake kokari kuma suna cin jarabawa na iya samun lalurar damuwa saboda tunanin yiwuwar rashin nasara.
Sakamakon Bincike:
Wannan ikirari ba gaskiya bane
Na biyar
Rashin kula mai kyau daga iyaye na haddasa lalurar damuwa ga yara.
Bincike:
Tabbas matsaloli irin talauci, rashin aikin yi, cin zarafi koma Kaura na iya haddasa lalurar kwakwalwa ga yara masu tasowa.
To amma an sha samun yara da suka fito daga gidan masu wadata, gidan da ake nuna musu so da kulawa amma suna fama da lalurar lafiyar kwakwalwa.
Sakamakon Bincike:
Wannan ikirari ba gaskiya bane. Duk mai lalurar lafiyar kwakwalwa mahaikaci ne, kuma ba’a warkewa.
Bincike:
Kungiyar likitocin halayya da tunanin mutane ta Amurka cikin bayanan data fitar na nuna alamomin lalurar kwakwalwa babu duka Ko hauka a ciki. Misali kungiyar likitocin halayya da tunani ta naje tace akwai akalla mutane miliyan 60 dake fama da lalurar kwakwalwa hakan ba yana nufin dukkansu haka bane. Haka zalika ana warkewa ta hanyar zuwa gurin masanan halayyar dan Adam da asibitocin kula da lafiyar kwakwalwa.
Sakamakon Bincike
Wannan ikirari ba gaskiya bane