Hukunci: Ƙarya ne
Binciken Alkalanci ta hanyar tuntubar ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso inda suka ce basu da masaniyar wannan labari. Sannan kasa samun wata sahihiyar kafar labarai data rawaito wannan labari ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin karya ne.
Takun sakar dake tsakanin shugaban kasar Burkina Faso da kasar Faransa ba abu ne boyayye ba.
Akwai dai zarge-zarge da dama kan kasar Faransa da ayyukan ta a wasu kasashen data raina wanda ya hada da Burkina Faso.
Akwai dai kalaman shugaban kasar na Faransa da yayi a kwanakin baya na cewa ya kamata kasashen da suka raina su godewa Faransa amma sai gashi sun sami akasin haka. Wadannan kalamai sun jawo cecekuce daga shugabannin kasashen da Faransa ta raina.
Tun bayan wannan jawabi ne dai ake samun labaran karya da ake alakantawa da shugaban Faransa ko kasar ta Faransa.
Wani shafin Facebook mai suna Hausawa (https://www.facebook.com/share/p/16eaav7KWa/?) ya wallafa wani labari dake cewa; Shugaban Faransa Macron ya sha alwashin ganin ya kubutar da Mutanen Burkina Faso daga hannun shugaba Ibrahim Traoré.

Wani shafin X wato Twitter mai suna @legitTargets (https://x.com/LegitTargets/status/1944313348239040615?t=zdpSDL1OkVuMgS2oYYQ-8Q&s=08)
Shi ma ya wallafa wannan ikirari.
Bincike:
Kasar Faransa dai ta kwashe dukkan sojojin ta daga kasashen Burkina Faso, Niger, Mali, Chad bayan da kasashen suka bukaci hakan.
Wannan sabon labarin dai ya fito ne daga shafin X din @LegitTargets wanda shafi ne kafafen tantance labarai da dama suka tantance labaran da shafin ke yadawa tare da samun shafin da yada labaran karya sosai.
Binciken Alkalanci bai samo wannan labari a kowanne irin sahihin shafin labarai ba na turanci ko na Faransanci.
Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyanawa Alkalanci cewa wannan labarin karya ne, domin babu wani abu makamancin haka da shugaba Macron ya fada.
Ma’aikatar ta kara da cewa wannan labari wani salo ne na masu yada labaran karya da bata sunan kasar Faransa a idanun mutane.
Alkalanci ta tuntubi wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Burkina Faso inda jami’in yace basu ga wannan labari ba. Ya ce tabbas ‘yan Burkina Faso sunyi murnar barin Faransa kasarsu amma bai san da wancan labarin ba.
Sakamakon bincike:
Kasancewar ba a sami wata sahihiyar kafar labarai data rawaito wannan labari ba, sannan musanta labarin da ma’aikatar harkokin wajen Faransa tayi da kuma ta kasar Burkina Faso da tace bata da masaniyar wannan labari, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan labari karya ne.
