Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da sojoji domin yakar ‘yan ta’adda wasu labarai suka cigaba da yaduwa na ƙarya.
Iƙirari:
Wani labari ya yaɗu matuka a kafar sada zumunta na Facebook yana iƙirarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya fitar da sanarwar cewa; “Ba iya yaƙar Nigeria kaɗai Zan yi Ba, Nayi Alƙawarin Mamaye ƙasar Baki ɗaya, Ba koda yaushe Muke Shiga Rikici don Mu Samu Nasara Ba Muna Shiga yaƙi don Mu Mamaye ƙasa, cewar Trump“.
Wani shafin Facebook mai suna Wakiliya ya wallafa wannan labari inda ya sami comments da shares da daruruwa.
Sannan shafukan Facebook kamar Dare Dubu Media ya wallafa haka zalika wani mai suna Alpu Hausa ya wallafa labarin inda dukkan su sun yi iƙirarin sun samo labarin ne daga “National Governors Association” a Melbourne, Florida.
Shafuka daban-daban sun wallafa wannan labarin tare da samun martani mai yawa daga jama’a na aibata shugaban ƙasar ta Amurka.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike mai zurfi kan wannan iƙirari domin gano gaskiyar lamarin.
Da farko, Alkalanci ta gudanar da bincike a manyan kafafen watsa labarai na duniya da na gida Najeriya kamar BBC Hausa, Al Jazeera, Daily Trust da sauransu, amma sun nuna babu ko da labari ɗaya mai kama da wannan.
Na biyu, binciken Alkalanci ya gano cewa tushen labarin da aka bayar (National Governors Association, Melbourne Florida) ba gaskiya ba ne. Sannan Helkwatar Ƙungiyar Gwamnonin Amurka (NGA) tana birnin Washington, D.C. ne, ba a Florida ba. Wannan yana nuna cewa an ƙirƙiri wurin ne domin bai wa labarin tuse na bogi.
Na uku, wannan ba shi ne karo na farko da ake yaɗa labaran ƙarya dangane da Trump da Najeriya ba. A baya, Alkalanci ta taɓa tantance wani labarin ƙarya makamancin wannan wanda ya yi iƙirarin cewa Najeriya ta bai wa sojojinta makamai don kai hari ga ƙasar ta Amurka, wanda aka tabbatar ba gaskiya ba ne. Wannan yana nuna cewa ana yaɗa labaran ƙaryar ne don tsoratar da jama’a.
Sakamakon Bincike:
Bisa la’akari da rashin samun wannan labari a sahihan gidajen jaridu, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan labari da shafukan Walkiya, Dare Dubu Media, da Alpu Hausa suka yaɗa ƙirƙirarre ne.
