BindiddigiLabaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

-

Hukunci: Ƙarya ne
La’akari da rashin samun wannan labari a sahihan kafafen yaɗa labarai na duniya da na gida, da kuma gano cewa ƙungiyar National Governors Association ba ta da mazauni a Florida kamar yadda labarin ya yi iƙirari, sannan duk shafukansu na yaɗa labarai ba su wallafa wani labari ba ko kusa da wannan, Alkalanci ya yanke hukuncin cewa iƙirarin da ke cewa Shugaba Donald Trump ya yi alƙawarin mamaye Najeriya ƙarya ne domin labari ne mara tushe.

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da sojoji domin yakar ‘yan ta’adda wasu labarai suka cigaba da yaduwa na ƙarya.

Iƙirari:
Wani labari ya yaɗu matuka a kafar sada zumunta na Facebook yana iƙirarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya fitar da sanarwar cewa; “Ba iya yaƙar Nigeria kaɗai Zan yi Ba, Nayi Alƙawarin Mamaye ƙasar Baki ɗaya, Ba koda yaushe Muke Shiga Rikici don Mu Samu Nasara Ba Muna Shiga yaƙi don Mu Mamaye ƙasa, cewar Trump“.

Wani shafin Facebook mai suna Wakiliya ya wallafa wannan labari inda ya sami comments da shares da daruruwa.

Sannan shafukan Facebook kamar Dare Dubu Media ya wallafa haka zalika wani mai suna Alpu Hausa ya wallafa labarin inda dukkan su sun yi iƙirarin sun samo labarin ne daga “National Governors Association” a Melbourne, Florida.

Shafuka daban-daban sun wallafa wannan labarin tare da samun martani mai yawa daga jama’a na aibata shugaban ƙasar ta Amurka. 

Bincike:

Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta gudanar da bincike mai zurfi kan wannan iƙirari domin gano gaskiyar lamarin.

Da farko, Alkalanci ta gudanar da bincike a manyan kafafen watsa labarai na duniya da na gida Najeriya kamar BBC Hausa, Al Jazeera, Daily Trust da sauransu, amma sun nuna babu ko da labari ɗaya mai kama da wannan.

Na biyu, binciken Alkalanci ya gano cewa tushen labarin da aka bayar (National Governors Association, Melbourne Florida) ba gaskiya ba ne. Sannan Helkwatar Ƙungiyar Gwamnonin Amurka (NGA) tana birnin Washington, D.C. ne, ba a Florida ba. Wannan yana nuna cewa an ƙirƙiri wurin ne domin bai wa labarin tuse na bogi.

Na uku, wannan ba shi ne karo na farko da ake yaɗa labaran ƙarya dangane da Trump da Najeriya ba. A baya, Alkalanci ta taɓa tantance wani labarin ƙarya makamancin wannan wanda ya yi iƙirarin cewa Najeriya ta bai wa sojojinta makamai don kai hari ga ƙasar ta Amurka, wanda aka tabbatar ba gaskiya ba ne. Wannan yana nuna cewa ana yaɗa labaran ƙaryar ne don tsoratar da jama’a.

Sakamakon Bincike:

Bisa la’akari da rashin samun wannan labari a sahihan gidajen jaridu, Alkalanci ta tabbatar da cewa wannan labari da shafukan Walkiya, Dare Dubu Media, da Alpu Hausa suka yaɗa ƙirƙirarre ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar