BindiddigiKo Gaskiya Ne Tinubu Ya Baiwa Faransa Damar Hakar...

Ko Gaskiya Ne Tinubu Ya Baiwa Faransa Damar Hakar Ma’adanai A Arewacin Najeriya?

-

Tun bayan da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ziyarci kasar Faransa akwai dai ikirari da labarai dake yaduwa wasu akwai kamshin gaskiya wasu kuma na karya.

Batu:

Wani shafin Facebook mai suna Lailu Hassan Moh’d ya wallafa wani bidiyo da a cikin bidiyo wani ke ikirarin cewa zuwan da shugaba Tinubu yayi zuwa Faransa ya sanya hannu kan yarjejeniya da Faransa na amincewa Faransa ta haki ma’adanan kasa a arewacin Najeriya.
Babban hadari a gabanmu in ba addu’a ba abinda zai tsallakar damu last week din nan da wanna mutumin Bola ya ziyarci Faransa ya gana da shugaban Faransa sunyi yarjejeniya cewa Najeriya zasu bawa Faransa arewacin Najeriya zasu zo su debi ma’adanai karkashin kasa.

Bincike:

Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa yayin ziyarar da shugaba Bola Tinubu yakai kasar Faransa ministan cigaban ma’adanan Najeriya ya rattaba hannu a madadin Najeriya kan batun bunkasa harkar ma’adana a Najeriya domin baiwa kasar damar raba kafa wajen hanyoyin shigar kudi.
Bayani daga ma’aikatar bunkasa harkar ma’adanai ya Najeriya tace yarjejeniyar ta kunshi batun hadin gwiwa wajen horaswa wato training, bincike wato research, da kuma musayar dalibai domin karin ilimi. Sannan yarjejeniya zata maida hankali kan yadda za’a sanya duk kamfanonin hakar ma’adanan kasa su kula da muhalli da rage amfani da injunan da suke gurbata muhalli.
Haka zalika yarjejeniya ta kunshi hadin gwiwa wajen sarrafa ma’adanai tare da tabbatar da cewa an kula da gururuwan dake kusa da guraren hakar ma’adanai kamar yadda yake a fadin duniya.
Ana kuma sa ran dawo da aiki a rijiyoyin ma’adanai dubu biyu da aka daina amfani dasu a sassana Najeriya.

Sakamakon Bincike:

Duk da cewa Najeriya da Faransa sun rattaba hannu kan batun ma’adanai to sai dai babu wani guri da aka bayyana cewa an baiwa kasar Faransa damar dibar ma’adanan kasa daga arewacin Najeriya kamar yadda mai ikirari yayi a wancan bidiyo. Kasancewar babu inda aka sami irin wannan bayani a rubuce ko a faifan sauti ko bidiyo dake nuna cewa an baiwa Faransa izinin dibar ma’adanai a arewacin Najeriya yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar