Hukunci: Ƙarya ne
Bisa bayanan hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO, hukumar kare yaduwar cututtuka da ma sauran hukumomin lafiya na duniya da suka bayyana cewa kashin Bera na haddasa cututtuka iri-iri misali zazzabin Lassa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin kashin Bera na maganin Appendix karya ne
Ikirari:
Akwai wani bidiyo mai tsawon sakan arba’in dake yaduwa a kafar sada zumunta ta Facebook da aka ji wani na ikirari cewa kashin bera yana maganin appendix.
“Ana samun kashin Bera a tara su da yawa, Idan aka tara sai a jika su a cikin ruwa, Idan aka jika ya jiku sai a rika bawa mai wannan shiwon yana sha. In dai yana sha Allah zai umarci wadannan tsakuwowin dake jikin sa su narke…)
Wannan bidiyo dai ya sami wadanda suka kalla sama da dubu ashirin.
Bincike:
Bera dai na cikin dabbobin da hukumomin lafiya suka sanya a matsayin mai yada cutuka zuwa ga mutum.
Hukumar lafiya ta duniya wato WHO tace kashi 60% na cututtuka masu yaduwa da aka fitar da bullar su a fadin duniya ana samunsu ne daga dabbobi. Haka zalika hukumar ta ce cututtukan da ake samu daga dabbobi na sanadiyyar mutuwar mutane miliyoyi kowacce shekara a fadin duniya.
Hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta bayyana cewa Bera na yada cutar zazzabin Lassa zuwa ga mutane, da zarar abincin da mutane suka ci ya gauraya da fitsari ko kashin Beran da ke dauke da kwayar cutar. Shi wannan Beran dai hukumar ta ce ana samun sa sosai a wasu kasashen yammacin Afrika wato harda Najeriya.
Zazzabin Lassa a Najeriya
Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce akalla mutane sama da dari biyu ne suka mutu sanadiyyar cutar zazzabin Lassa a shekarar 2024.

Hukumar ta gargadi mutane da su guji cin Bera ko kuma barin kayayyakin abinci a bude inda Bera ka iya yin kashi ko fitsari a ciki.
Kungiyar bada tallafin magungunan riga kafi ta Gavi ta ce akalla mutane miliyan biyu da dubu dari bakwai ne ke kamuwa da zazzabin Lassa a duk shekara.
Masu bincike kan harkar lafiya sun bayyana cewa kashin Bera na da matukar hadari domin yana iya yada cututtuka sosai, musamman masu yaduwa wanda ka iya haddasa asarar rayuka.
Babu dai inda a kimiyyance aka ce kashin Bera na da wani magani fyace cutarwa.
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanan hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO, hukumar kare yaduwar cututtuka da ma sauran hukumomin lafiya na duniya da suka bayyana cewa kashin Bera na haddasa cututtuka iri-iri misali zazzabin Lassa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin kashin Bera na maganin Appendix karya ne.
