BindiddigiKarya ne Ali Nuhu bai samar da Asibiti a...

Karya ne Ali Nuhu bai samar da Asibiti a Abuja ba

-

Hukunci: Ƙarya ne
Ali Nuhu ya tabbatarwa Alkalanci cewa karya ne bai samar da asibiti mallakinsa a Abuja ba. Kuma binciken Alkalanci ya tabbatar da samun hoton da ake yadawa na kirkirarriyar basirar AI ne, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin da hotunan da ake yadawa cewa Ali Nuhu ya samar da cibiyar kula da lafiya dauke da sunan shi a Abuja karya ne.
Akwai dai wani labari da kuma hotuna dake matukar yaduwa a kafafen sada zumunta dake ikirarin cewa shahararren dan wasan kwaikwayo Ali Nuhu ya samar da cibiyar kula da lafiyar mutane wato Medical center a Abuja.
Hoton wanda aka rubuta Sarki Ali Nuhu Medical Center Abuja.
Akwai dai wannan shafin Tiktok din ((https://vm.tiktok.com/ZSShHhYGX/)) wanda yayi ikirarin cikin asibitin.
Labarin karya dake Cigaba da yaduwa
Sannan akwai shafuka da dama a Facebook da suka yada wannan labari. ((https://www.facebook.com/share/1Pyr534fdK/?mibextid=wwXIfr))
Dukkan shafukan dai na wallafa hoto da kuma rubutu kamar haka “ SARKI  ALI NUHU MEDICAL CENTRE ABUJA.”
Labarin karya dake cigaba da yaduwa
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntubi Ali Nuhu kai tsaye inda ya bayyana cewa ba gaskiya bane domin shi bai bude wani asibiti ko cibiyar lafiya ba. “Tabbas na ga wani hoton da akayi da kirkirarriyar basirar AI da ake cewa asibiti na ne da na bude a Abuja.”
Haka zalika kafar Alkalanci ta sanya hoton kan manhajar duba hotunan da akayi da kirkirarriyar basirar AI inda manhajar ta tabbatar da cewa hoton hadin AI ne.
Ali Nuhu dai baya ga kasancewar sa gwarzon dan wasan kwaikwayo a yanzu haka shine shugaban hukumar harkokin fina-finai ta Najeriya wato Nigeria Film cooperation.
Sakamakon bincike:
Bisa bayani daga bakin Ali Nuhu inda ya musanta samar da asibiti mallakinsa a Abuja, da kuma tabbatar da samun cewa hoton da ake yadawa na kirkirarriyar basirar AI ne, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin da hotunan da ake yadawa cewa Ali Nuhu ya samar da cibiyar kula da lafiya  dauke da sunan shi a Abuja  karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar