Akwai wani shafin TikTok mai suna @Yakuburasha42 ya wallafa wani faifan bidiyo dake iƙirarin cewa gadar data hada Gombe da Adamawa ce ta karye a ruwan da akayi ‘yan kwanakin da suka gabata.
((https://vm.tiktok.com/ZSAFrL67N/))
A cikin bidiyon an jishi yana roƙon masu amfani da kafar sada zumunta ta Tiktok da su taya su da addu’a. “Salamu alaikum jama’ar Tiktok ku saka mu a addu’a gamunan dai kamar yadda kuke gani nana ne hanyar Gombe to Adamawa kwalta ya yanke wallahi, gashinan dai ba halin mutum ya wuce. Wallahi kwalta ya rigada ya yanke ruwa ya fasa shi.”
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta sanya wani sashe na bidiyo a inda za a iya gano ko an taba amfani da bidiyo ko hoto, sakamakon ya fito da irin wannan bidiyo a wasu shafuka, sunyi amfani da shi a watan Satumbar shekarar 2024. Cikin shafukan da sukai amfani da afkuwar karayewar gadar da ka nuna a wannan bidiyo har da gidan jaridar talabijin na Trust TV. (https://youtu.be/HSiC10NCMMw?si=XYdEfS456j-V1txn)
Sakamakon bincike:
Bisa samun wannan bidiyo a matsayin tsohon bidiyo wato abin ya faru a shekarar data gabata ne yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa yaudarar mutane ake son yi wato misleading a turance.
