Hukunci: Ƙarya ne
Bisa kasa samun labarin ko bayanin cewa shafin na Whatsapp ya fara biyan kuɗi ko kuma ace yana biyan kuɗi kyauta. Kafar ta WhatsApp dai ta bada damar tura ko karbar kudi ta hanyar hadin gwiwa da wasu bankuna. Idan kafofin sada zumunta zasu ko kuma sun fara biyan masu amfani da shafin nasu, suna sanar da wannan manufa. To amma ya zuwa yanzu babu wata sahihiyar kafa data ruwaito wannan labari. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne.
A ƴan kwanakin nan ne dai wasu bidiyo ke yaɗuwa matuƙa inda wasu ke iƙirarin cewa kafar tura saƙwanni ta Whatsapp ya fara biyan kuɗi kamar yadda wasu shafukan suke biyan masu amfani dasu.
Iƙirari:
Shafukan daban-daban dai na iƙirarin cewa mutane na samun dubunnai Nairori wasu ma na cewa miliyoyi Nairori kyauta ta amfani da Whatsapp.

Duk mutanen da sukai magana a bidiyon dake shafukan na Tiktok dai na cewa mutane su danna ko su shiga link din dake bio ko ƙasan bidiyon.
Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta duba shafin yanar gizon na Whatsapp inda bata ga no inda kafar tace ta fara abinda ake cewa monetization wato samun kuɗi daga shafin.
Shafin dai ya nuna cewa a yanzu an iya tura ko karbar kuɗi ta Whatsapp din domin sun ƙulla alaƙa da wasu bankuna.

Duk da cewa idan mutum yana sayar da wani abu ko tallan abubuwa mutum na iya samun kuɗi amma dai ya zuwa yanzu Whatsapp bai fara biyan masu amfani dashi ba.

To amma dai Alkalanci bata tabbatar da cewa wanda ke Najeriya zai iya amfani da wannan hanya wajen tura kudi ko karbar kudi ba.
A kasashe irin su India mutum na iya siyen tikitin jirgin kasa ta amfani da WhatsApp.
Sakamakon bincike:
Bisa kasa samun labarin ko bayanin cewa shafin na Whatsapp ya fara biyan kuɗi ko kuma ace yana biyan kuɗi kyauta. Idan kafofin sada zumunta zasu ko kuma sun fara biyan masu amfani da shafin nasu, suna sanar da wannan manufa. To amma ya zuwa yanzu babu wata sahihiyar kafa data ruwaito wannan labari. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin ƙarya ne.
