BindiddigiIna gaskiyar cewa Faransa ta koma siyen Uranium daga...

Ina gaskiyar cewa Faransa ta koma siyen Uranium daga Rasha bayan barin Nijar?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Kasancewar binciken Alkalanci ya gano cewa kamfanonin kasar Faransa na siyen Uranium daga Rasha tuntuni, kuma sun rage siya daga Rasha tun daga shekarar 2022, sannan kuma akwai ƙasashe da dama da Faransa ke siyen Uranium a hannun su shekara da shekaru. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin dake cewa Faransa na rokar Rasha ta siyar mata da Uranium saboda an koreta daga Nijar ƙarya ne.

Tun bayan hamɓarar da gwamnatin shugaba Muhammadu Bazoum da sojin kasar Nijar sukayi, aka sami takun saƙa tsakanin gwamnatin sojin ta Nijar da ƙasar Faransa.
Hukumomin Nijar sun kori kamfanin haƙar ma’adanai na ƙasar Faransa, tare da yanke hulɗar siyar da uranium ma kamfanin na ƙasar ta Faransa.

Bayan hakan ne iƙirarai kala-kala ke yaɗuwa na cewa Faransa ta rufe tashar Nukilyar ta, wasu kuma na cewa Faransa na tsaka mai wuya kan batun ƙarancin uranium saboda korar da aka musu daga Nijar.

Iƙirari:
Wani shafin Facebook mai suna Aboubakar Mara ya wallafa wani bidiyo inda yake iƙirarin cewa ƙasar Faransa ta koma siyen Uranium daga Rasha bayan da Nijar ta kore ta.
“Faransa tayi tauri Janaral Tchiani ya rufe urani din Nijar yanzu daga Rasha suka koma suna karamar murya, don a saida musu Uranium.”
((https://www.facebook.com/share/r/16nSTorWXi/?mibextid=wwXIfr))

Bincike:
Tun kafin a yi juyin mulkin ƙasar Nijar dai ƙasar Faransa da tarayyar Turai wato EU suke siyen makamashin Uranium daga kamfanin ƙasar Rasha mai suna Rosatom wanda shine kan gaba wajen sarrafa uranium a duniya.
To sai dai bayan da Rasha ta fara mamayar ƙasar Ukraine, kamfanin uranium na Faransa da kuma kamfanonin Tarayyar Turai suka ayyana rage siyen uranium daga kamfanin na ƙasar Rasha.
((https://www.euronews.com/business/2023/10/20/))

Haka zalika ƙasar ta Faransa tun kafin wannan taƙaddama, ƙasar Nijar ba ita bace kan gaba wajen samarwa da Faransa Uranium, domin tana siya daga ƙasashe da dama irin su Kazakhstan, Australia da sauran su kamar yadda bayanan bankin duniya ya nuna.
((https://wits.worldbank.org/trade/comtrade/en/country/FRA/year/2023/tradeflow/Imports/partner/ALL/product/284410))
Bincike ya nuna cewa zuwa yanzu dai kamfanin kasar Faransa na siyen Uranium daga Rasha duk da cewa ya ragu matuƙa, yayin da kamfanin ke shirin daina siyen Uranium daga kamfanin ƙasar Rasha nan da shekaru uku wato 2028. A cewar wani rahoto.
((https://bellona.org/news/nuclear-issues/))

Sakamako bincike:
Kasancewar binciken Alkalanci ya gano cewa kamfanonin kasar Faransa na siyen Uranium daga Rasha tuntuni, kuma sun rage siya daga Rasha tun daga shekarar 2022, sannan kuma akwai ƙasashe da dama da Faransa ke siyen Uranium a hannun su shekara da shekaru. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin dake cewa Faransa na rokar Rasha ta siyar mata da Uranium saboda an koreta daga Nijar ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar