Sanya hijabi dai dabi’a ce ta Musulman duniya wanda ya hada harda Najeriya. Shekaru da dama dai Musulman Najeriya na sanya hijabi domin cika umarnin Allah da manzan sa.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna Safiyya Aliya ta wallafa wani hoto mai dauke da rubutun ikirarin cewa matar shugaban kungiyar Shi’a wato Ibrahim El-Zakzaky itace ta fara sanya hijabi a kasar Hausa. “Bincike ya nuna cewa uwar gidan Sheikh El-Zakzaky ita ce ta fara sanya hijabi a kasar Hausa”
Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta fara da bincikar batun sanya hijabi a kasar Hausa, inda ta gano cewa Hausawa musulmi na amfani da mayafi, gyale a matsayin hijabi kamar yadda addinin musulunci ya umarci mata su lullube jikinsu.
Duk da cewa a Hausance akwai banbanci tsakanin Hijabi da mayafi ko gyale to amma dai akwai rubuce-rubuce na malaman addini a kasar Hausa da suka bayyana wasu daga cikin mayafi ko gyalen da matan Hausawa ke sawa a matsayin hijabi musamman Idan ya cika sharrudan da addini ya shar’anta na rufe jiki.
Akwai wani bincike da aka wallafa a wani shafi mai suna African studies Center kan hijabi a arewacin Najeriya ko ace kasar Hausa. Binciken ya banbance tsakanin mayafi, gyale, layafa da hijabi inda binciken yace ana sanya hijabi a arewacin Najeriya amma an fara sanya hijabi ne sosai a farko-farkon shekarun 1970s. Binciken ya anbato kokarin marigayi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi wajen batun sanya hijabi ya zama ruwan dare yanzu a arewacin Najeriya .
Sannan kafar bincike da bindiddigi ta Alkalanci ta gano cewa dadewar hijabi a kasar Hausa kamar dadewar musulunci ne a kasar Hausa.
Haka zalika kafar Alkalanci ta tuntubi Ibrahim Musa wanda shine babban editan jaridar Almizan wacce take mallakin mabiya Shi’a kan gaskiyar wannan ikirari da aka alakanta da matar jagoran kungiyar Shi’a inda yace “Salam. Ban san wanne irin bincike suka yi ba. Kuma wane irin ma’aunai suka yi amfani da shi ba wajen yin wannan ikirarin. Na san dai ‘yan’uwa ne ke fadin haka.
Amma ni a ganina zai yi wuya hakan ya zama gaskiya, saboda hijabi wani abu ne da yake cikin Musulunci. Musuluncin nan kuma akwai shi a kasar nan tun kan a haife mu.”
Sakamakon Bincike:
Bisa iya dogon bincike da kafar Alkalanci tayi na ma’anar hijabi da kuma sanya shi a kasar Hausa da kuma bincike da ma’abota ilimi sukayi babu inda aka ambato takamaimai lokacin da aka fara sanya hijabi a kasar Hausa balle wacce ta fara sanyawa.
Haka zalika batun hijabi kasancewar umarni ne na musulunci wanda musulunci ya dade matuka a kasar Hausa, kuma matan musulmi a kasar Hausa na rufe jikinsu kodai lokacin yin sallah ko zuwa unguwa tun shekaru aru-aru. Wanna yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.