Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun bayanin ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen ƙasar Burkina Faso na ƙaryata wannan labari tare da bayanin cewa labarin ya daɗe yana yawo tsakanin mutane, kuma Saudiyya bata gabatar da wannan bukata ba. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa, iƙirarin cewa ƙasar Burkina Faso tayi watsi da buƙatar Saudiyya na gina masallatai 200 ƙarya ne.
Iƙirari:
Akwai wani shafin Facebook mai suna Comr Abba Sani Pantami ya wallafa wani iƙirari a ranar 20/03/2025 dake cewa; “Shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Traore ya ki yarda da bukatar Saudiyya na gina masallatai 200 a kasarsa yace a madadin haka a yi amfani da kudaden wajen gina masa kamfanoni da koyawa matasan kasarsa sana’o’i da ayyukan dogaro da kansu.”
Wannan post dai ya sami tofa albarkacin baki wato comments sama da dubu ɗaya.

Wani shafin Facebook mai suna Damagaram post shima ya wallafa wannan labarin.
Wannan labari ya sami tofa albarkacin baki sama da dari shida.

Har ila yau wani shafi mai suna A Yau shima ya wallafa wannan labari.
Wannan wallafa ta sami tofa albarkacin baki sama da dubu ɗaya da ɗari shida.

Bincike:
Kafar tantance labarai bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta tuntuɓi ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta Burkina Faso inda jami’in ma’aikatar yace mu duba shafin Facebook ɗin ma’aikatarinda Alkalanci ta samo bayanin ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen ta Burkina faso da ta wallafa a ranar 20 ga watan Maris 2025 inda ta ƙaryata wannan labari dake yaɗuwa na cewa ƙasar Saudiyya ta wa Burkina Faso alƙawarin gina masallatai 200 wanda ita ƙasar tayi watsi da wannan buƙata.
Bayanin ya ƙara da cewa wannan rubutu an fara yaɗa shi tun a shekarar 2023, wanda ya ƙara dawowa a wannan shekarar ta 2025.
Ma’aikatar tace tun 2023 ta ƙaryata labarin, wanda bisa lura da yadda ya cigaba da yaɗuwa yasa dole aka ƙara fitar da sabuwar sanarwa.


Sakamakon bincike:
Bisa samun bayanin ma’aikatar harkokin ƙasashen wajen ƙasar Burkina Faso na ƙaryata wannan labari tare da bayanin cewa labarin ya daɗe yana yawo tsakanin mutane, kuma Saudiyya bata gabatar da wannan bukata ba. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa, iƙirarin cewa ƙasar Burkina Faso tayi watsi da buƙatar Saudiyya na gina masallatai 200 ƙarya ne.
Labarai masu alaka: