Garin Falgoren Daji dake karamar hukumar Doguwa gari ne dake bakin dajin daya hada jihar Kano da Bauchi kuma ya hade da dajin Yankari. Gari ne dake da kasuwa inda ake siye da siyarwar kayan noma da dabbobi.
Batu:
Akwai wani ikirari da wani shafin Facebook mai suna RFI Hausa ya wallafa wani bidiyo mai tsawon mintuna biyu tare da rubuta cewa wata mata dake bidiyon itace mace ta farko data kammala karatun digiri a yankin Falgore karamar hukumar Doguwa dake jihar Kano.
“ Mace ta farko da ta kammala karatun digiri a yankin Falgore dake karamar hukumar Doguwa a jihar Kanon Najeriya.”

Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta fara bincika kafin ita wannan mata a bidiyo da akai ikirari akwai mace ‘yar wannan gari ta Falgore data kammala karatun digiri? Alkalanci mun gano cewa akwai mata da suka kai akalla hudu da suke yan asalin wannan gari na Falgore ne kuma sun kammala karatun digiri shekaru kafin ita wacce aka wallafa a bidiyon wacce ko hidimar kasa wato NYSC ma batayi ba.
Mun tuntubi wani dan asalin wannan gari na Falgore kuma ma’aikaci a jami’ar ABU mai suna Nuraddeen Adam Iliyasu wanda yace; “Akwai mata ‘yan asalin garin Falgore da suka kammala jami’a. Ina farin ciki cewa ita wannan mata mai suna Asiya ‘yar garin namu na Falgore ta kammala digiri amma batun cewa ita ta farko bai taso ba.”
Ga sunayen wasu daga cikin matan da ‘yan asalin wannan gari na Falgore ne, kuma sun kammala karatun digiri.
- Hadiza Ibrahim BSc. Adult Education 2018
- Halima Ibrahim Yusuf BSc. Nursing (BUK)2021
- Bushira Garba Abdu B.Ed (ABU)2023
- Hajara Ibrahim BSc. English (BUK)2020
Ya kara da cewa, “dukkan su Idan anzo karbar tallafin karatu wato scholarship takardun shaidar gari na asali dama karamar hukuma duk na Falgore da karamar hukumar Doguwa ne.”
A ikirarin ance yankin Falgore wanda hakan ke nufin garuruwan dake kusa da Falgore inda Nuraddeen ya kara da cewa; “Yankin Falgore suna nufin Idan ka hauro daga daji kenan, to ya zasuyi da mata da yawa da suka kammala digiri ‘yan asalin garin Burji?”
Sakamakon Bincike:
Bisa samun bayani daga ‘yan wannan gari tare da tabbatar da cewa wadancan sunaye ‘yan asalin wancan gari na Falgore ne, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin RFI Hausa na cewa Asiya itace mace ta farko data kammala digiri daga yankin Falgore karya ne.