BindiddigiIna Aka Kai Yaran Da Ake Zargi Da Cin...

Ina Aka Kai Yaran Da Ake Zargi Da Cin Amanar Kasa?

-

Ranar Juma’a ce dai gidajen jaridu da kafafen sada zumunta suka cika da labari, hotuna da bidiyo na wasu yara da hukumar ‘yan sanda ta Najeriya ta gurfanar a wata kotu a Abuja kan zargin cin amanar kasa bisa shiga zanga-zangar tsananin rayuwa da rashin shugabanci na gari da akayi a watan Augusta.
An dai ga hotuna da bidiyon yaran yankwane har aka hangosu suna wawar biskit.
Tun bayan fitowa wannan labari da hotuna ne dai ‘yan Najeriya ke tofa albarkacin bakinsu. Cikin manyan kasar da suka caccaki wannan batu harda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar inda ya bayyana wannan abu da rashin tausayi kan kananan yara.
Wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama ma sunyi Allah wadai da wannan mataki na tsare yaran tare da sanya miliyan goma a matsayin kudin beli ga kowanne yaro.
Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bada belin yara 67 cikin 76 beli kowannen su ya biya miliyan goma.
Yayin da cikin wadanda basu kai shekaru 15 ba zasu gabatar da wanda zai tsaya musu kuma dole ya kasance ma’aikacin gwamnati.

Lauyan Gwamnati:

To sai dai a zantawa da manema labarai lauyan gwamnati Barista Rimazonte Ezekiel yace “Wadannan yara da muka kawo kotu yau dukkansu balagaggu ne, mafi yawancin su suna da aure babu wanda bai balaga ba a cikin su, wasunsu ma sun kammala jami’a kananan yaran kuka gani sunzo ne da iyayensu domin su gaida wadanda suke kauna (iyayensu) ba sune aka kama kuma ake zargi a wannan batu ba. Wadannan yara an kamasu ne a Zariya da Kaduna…. Mun shigar da kara kan mutane 43 kuma sun gurfana a gaban kotu yau kuma dukkansu balagaggu ne ku manta da abinda da su lauyoyin wadanda ake kara suke fada muku cewa kananan yara ne shin sunma san wadanda suke karewa?

Me Yansanda Suka ce? 

Bayan lauyan gwamnati ya karyata batun cewa wadanda aka gurfanar ba kananan yara bane to sai kuma mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ya fitar da sanarwar inda Sanarwar ta bayyana cewa an gurfanar da wadanda ake zargi su 76 harda kananan yaran tsakanin shekaru 12 zuwa 15 gaban kotu kan zargin cin amanar kasa da kokarin kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta hanyar shiga zanga-zanga. Sanarwar ta kara da cewa an kama yaran tun 3 ga want August 2024 wato watanni uku kenan.
Sanarwar ta kara da cewa suman da wasu daga cikin yaran sukayi shiryenyen abune?

Gidan Yari?

Tunda aka kama yaran a watan Agusta suke hannun yan sanda.
Daya daga cikin lauyan yaran Barista Deji Adeyanju dai ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa tuni an garzaya da yaran zuwa gidan gyara hali na Kuje.
Baya ga shi Deji mutane da dama sun wallafa cewa an tasa keyar yaran zuwa gidan gyara halin na Kuje duk da cewa wasu na ganin ya sabawa doka.

Me Hukumomin Gudajen Gyara Hali Na Najeriya Ke cewa?

Alkalanci ya tuntubi mai magana da yawun hukumar gyara hali ta Najeriya Abubakar Umar inda yace “Batun cewa mun karbi yara kanana a wasu daga cikin gidajen gyara hali ba gaskiya bane domin Muna aiki cikin kwarewa kamar yadda yake a duk fadin duniya. Ina tabbatar maka cewa Kasancewar dokar kafa gidajen gyara hali ta shekarar 2019 ta baiwa shugabannin dake kula da wadannan gidaje da Kada su karbi yaran da basu balaga ba, ko kuma Idan gidajen babu guri.  Don haka babu wani wanda bai balaga ba da muke tsare dashi musamman kan wannan batu na wadannan yara da ake zargi da zanga-zanga.”
Akwai dai bayanin cin karo da juna tsakanin biyanan na ‘yan sanda da kuma shi lauyan gwamnati.

Ga dai sunayen wadanda aka gurfanar da shekarun wasu daga cikin su bisa alkaluman ‘yan sanda da wanda aka gabatar.

Nura Ibrahim shekaru 24 , Abdulbasi Abdusalami, Ahmed Yusuf 25, Awolu Abdulahi 21, Umar Musa 15, Muhammadu Mustapha 16, Umar Muhammed 23, Umar Inusa 18, Abdullahi Sani 21, Abba Usman, Ibrahim Rabiu 16, Abubakar San, 19, Abubakar Abdullahi 18, Amir Muhammed 17, Umar Ali 17, Saminu Sani 22, Muhammed Musa 14, Suleiman Dauda 18, Ismail Abdullah 27 da kuma Haruna Suleiman 22.

Sauran sune Bello Abdullahi 23, Usman Yunusa 20, Umar Umar 25, Sani Aliyu 17, Yusuf Lawal 21, Abba Adamu 22, Abbas Hamza 20, Tasiu Lawal 16, Jamilu Haruna 16, Usman Mohammed 20, Aminu Usaini 20, Aminu Mohammed 24, Abdullahi Suleiman 16, Bilal Auwalu 15, Umar Kabir 22, Abubakar Ibrahim 18, Usman Yusuf 22, Abubakar Adam 16, Suleiman Ali 16, Mubarak Hamza 23, Ibrahim Musa 24, Samani Ali 25, Yahaya Sani 20, Umar Sani 26, Abbas Haliru 24, Sani Idris 17, Tashiru Mohammed 18, Abdulaziz Abubakar 15, Usman Sirajo 16 da kuma Musa Adam 22.

Akwai kuma; Mukhtari Yahaya 17, Abba Ahmad 23, Umar Mohammed 24, Yahaya Musa 18, Umar Abdullahi 17, Salisu Adamu 16, Habibu Sani 17, Sadiq Sanusi 15, Ibrahim Sani 17, Mustapha Kabir 16, Saifullah Mohammed 17, Hassan Mohammed 17, Mustapha Abubakar 17, Sanusi Nura 14, Abdulmalik Auwal 19, Musa Ishaku 17, Abdulrahman Ibrahim 17, Usman Ibrahim, Usman Fatihu 21, Abdulganiu Musa 15, Sagir Hassan 19, Saidu Usman 25, Abubakar Muhammed 22, Kabiru Sani 25, Muhammed Yahaya 14, Mukhtar Alhassan 16, and Mustapha Ibrahim 18.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Ina gaskiyar cewa Amurka, Faransa ke neman haddasa faɗa tsakanin Sudan da Chadi?

  Duk lokacin da aka sami wata hatsaniya ko rikici tsakanin kasashe, wasu na amfani da wannan dama wajen yada...

Bidiyon ƴan sanda sunyi kame a Edo ƙarya ne, bidiyon ya faru a Ghana ne

  A yayin da ƴan Najeriya ke cigaba da Allah wadai da kisan wasu matafiya a jihar Edo, wasu na...

Karanta wannan

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar