Yayin da hukumomin jihar California ke cigaba da kokarin shawo kan wutar dajin dake ci a jihar, ikirari, hotuna da bidiyoyin karya na cigaba da yaduwa a kafafen sada zamunta.
Batu:
Wani shafin sada zumunta na Facebook mai suna SHURA TV ya wallafa wani ikirari (archived here) tare da hoto inda yake rubuta; “ Aya Daga Cikin Ayoyin Ubangiji Madaukakin Sarki. Gidan Wani Musulmi da Suke Karanta Alqur’ani Mai Girma da Wutar Los Angeles dake Amerika ta Tsallake Bata Taɓa ba. Allah ka Tsallakar da Muslimi Daga Musifar Duniya da da Lahira.”
Hoton ƙarya dake cigaba da yaduwa
Shima wani shafi na Facebook mai suna Muhammed Mustapha Yahuza Kumurya ya wallafa irin wancan hoto (archived here) tare da rubuta “ Wllh ko iya wannan Ya isheku, kuduba kuga yadda wutar daji da takecigabada CI A chan birnin los angeles yadda ta hallake wani gida guda daya da ake yawan karatun Alqur,ani. Allah yakarakare Addinin musulunci da musulmi baki daya.”
Hoton ƙarya dake cigaba da yaduwa.
To amma wani shafin na Facebook mai suna Karaduwa Post Hausa hotuna biyu ya wallafa kowanne daban (archived here) tare da ikirarin cewa “ ALLAH AKBAR: Kalli Duk irin wutar da cinye birnin Los Angeles Kasar Amurika, amma cikin ikon Allah wutar ta tsallake gidan da ake karantar Da Al-Qur’âni mai girma.”
Hotunan ƙarya dake cigaba da yaduwa
Bincike:
Binciken kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa hoton da SHURA TV, Muhammed Mustapha Yahuza Kumurya suka wallafa gida ne da akayi da itace mai shekaru dari a garin Lahaina dake Hawaii lokacin da aka sami wutar daji data kone gidaje kusa dashi a shekarar 2023.
Haka zalika binciken Alkalanci ya gano cewa gidan bashi da alaka da kowanne addini.
Hoton labarin wutar 2023.
Daya daga cikin hotunan da shafin Karaduwa post Hausa ya wallafa inda bayan sanya hoton a manhajar duba sahihancin hoto inda sakamako ya nuna cewa hotone da akai amfanin da kirkirarriyar basira AI wajen hadashi.
Sakamakon bincike:
Bisa gano cewa hoto na farko tsohon hotone na wutar daji a Hawaii a shekarar 2023 a yayin dana biyu kuma kirkirarren hoto ne da aka hada. Kafar Alkalanci ta yanke hukuncin cewa iƙirari ƙarya ne.