Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun asalin bidiyon hoton wacce akai ikirarin ita ce ke fuskantar shari’a kan ridda a jihar Zamfara wanda kuma Alkalanci ta ga no cewa wacce ke hoton da ake yadawa ita musulma ce wacce ta karbi musulunci a baya kuma ba a Najeriya ta ke zaune ba, tana kasar Amurka ne. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa hoton karya ne akai amfani da shi.
Shafin Sahara reporters ya fara wallafa labari da hoton wata budurwar inda shafin yace ita ce kw fuskantar shari’a a kotun musulunci kan ridda. amma daga baya ya goge hoton bayan awanni.

Wani shafin mai suna daily post ya wallafa labarin a ranar 20 ga watan Yunin 2025 inda ya bayyana cewa wata budurwa a Zamfara na fuskantar sharia a kotun musulunci saboda yin ridda zuwa addinin kirista. Shafin ya sanya hoton wata budurwa mai duhun fata a matsayin ita ce.

Wani shafin ma mai suna intelregion shima ya wallafa wannan hoto da kuma labarin inda sh yace budurwa yar shekaru 22 mai suna Zainab Muhammadu na fuskantar hukuncin kisa saboda yin ridda.

Bincike:
Kafar tantance labarai ta gano wacce aka sanya hoton inda ta kasance daya daga cikin masu amfani da kafar sada zumunta wajen yin bidiyo da maganganu mai amfani da sunan Aalia Reeves. Shafinta na Instagram @aaliaa_reeves shafin TikTok @Aaliareeves.

Bidiyon da aka dauki hoton dai ta wallafa shi a shafin ta na Instagram tana magana kan yadda take fama da mahaifiyarta tun bayan da ta karbi addinin musulunci.
Ta bayyana yadda a wasu lokuta mahaifiyarta wacce kirista ce take taimaka mata a wasu lokutan kuma take kin bata hadin kai. Ta kara da cewa ta sanya kawayenta da suka je Umrah da su sanya mahaifiyarta a addua.
Ita dai wacce akai amfani da hoton nata ba ma a Najeriya ta ke zaune ba. Tana kasar Amurka ne.

Gwamnatin jihar Zamfara ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Sulaiman Bala Idris ta ce babu wata Zainab Muhammadu wacce ke fuskantar shari’a saboda ridda a jihar ta Zamfara.
Sakamakon bincike: