Masallacin kasa wato National Mosque dake Abuja dai gurin ibadane da mafi kasarin lokuta shugabanni ke zuwa yin ibada ko daura auren ‘ya’yansu.
Batu:
Ranar Juma’ar data gabata ne dai aka hango shugaban Najeriya, Bola Tinubu, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, wanda ba musulmi ba, kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da sauran manyan mutane a zaune a sahun gaba a masallacin kasa.
Bayan bullar wannan hoto ne dai aka farun samun masu tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu inda wani mai amfani da Facebook mai suna Shehu Tijjani Shareef
ya rubuta cewa (archived here) “Akpabio a Masallaci Muslim-Muslim ta fara muluntar da jami’an gwamnati.”
Wannan wallafa ta sami mutane da dama da suka tofa albarkacin bakinsu tare da aminta da abinda ya rubuta misali; Imrana Auwal Dan So yace “Masha Allah mulkin Tinubu anci riba sosai.”
An dai sami ire-iren wannan wallafa dake nuna cewa shugaban majalisar dattawa Akpabio yayi Sallah a sahun gaba. Misali wani mai suna Muhammad Tukur Usman yace (archived here)“ Wato magana ake ta Mulki Kawai a Abuja😀😀 Senate President ne a Masallaci( Godwin Akpabio) Kuma a sahun gaba.“
Shima Sa’ad Matawalle cewa yayi (archived here) “Babban cigaban da muslim muslim ticket ta kawo shine shiga da AKPABIO cikin masallaci.🙄😭“
Bincike:
Binciken Alkalanci ya gano cewa shugaban majalisar bai shiga masallacin don zama musulmi Ko yin Sallah ba fyace yaje domin shaida daurin auren yar Sanata Danjuma mai suna Fauziyya.
Sakamakon Bincike:
Bisa binciken da Alkalanci yayi ya tabbatar da cewa zuwan Sanata Akpabio Masallacin Kasa da zama a gaba bashi da alaka da ibadar sallah Ko zama musulmi face shaidar daurin auren ‘yar daya daga cikin Santocin daya ke jagoranta. Wannan yasa ikirari ya zama karya wato false a turance.