Hukunci: Ƙarya ne
Bisa samun cewa akwai shafi ko asusun Instagram da Ameena Dikko Radda ta buɗe tun 2018, kuma tayi verifying dinsa a 2025, tare da samun cewa mahaifiyarta Zulaihat Abdullahi Dikko na binta suka tabbatar da cewa Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin gwamnatin Katsina na cewa bata da wani shafin sada zumunta kwata-kwata ƙarya ne.
Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka nuna tare da wallafa wasu hotuna dake cewa tana neman kujerar Sanata a jahar Katsina kamar yanda kuke gani a wanna hoton.
Waɗannan hotuna dai sun yaɗu matuƙa a kafafen sada zumunta musamman Facebook.
Iƙirari:
Wani shafin Facebook ya wallafa hoton ‘yar gwamnan dake nuna cewa zata nemi kujerar Sanata a Jihar Katsina a cikin wani zaure wato group.
Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da sanarwa a hukumance, inda ta karyata wannan zargi baki daya, tare da bayyana cewa shafin da ake yadawa na bogi ne.
Sanarwar gwamnatin yayi iƙirarin cewa ƴar Gwamna Radda ba ta neman kowacce kujera ta zabe ,har Ila yau sun kara da Sanar da cewa , ba ta da shafin Facebook ko ma wani shafin sada zumunta kwata-kwata.
Wasu manyan gidajen jaridu na Hausa sun rawaito wannan labari misali Arewa Update da kuma DCL.
Yayin da gwamnatin ta ƙaryata wancan labari sai kuma mutane suke tambayar anya gaskiya ne Ameena Dikko Radda bata da wani shafin kafar sada zumunta?
Wannan yasa Alkalanci zurfafa bincike wajen gano gaskiyar labarin cewa shin Ameena Dikko Radda bata da shafi a kafafen sada zumunta kamar yadda gwamnatin jahar Katsina ta bayyana?
TikTok:
Da farko dai Alkalanci ta fara da Duba kafar TikTok inda tasamu shafuka sama da 50 da suke amfani da sunan Amina Dikko Radda ba tare da samun wani gamsasshe da za a iya cewa nata ne ba. Wato dai Alkalanci bata sami ɗaya da zata iya alaƙanta shi da Ameena Dikko Radda ba.
Facebook:
Haka zalika Alkalanci ta garzaya Facebook inda shima aka samu shafuka da dama da suke amfani da sunan ƴar gwamna Radda.
Akwai wani shafin main suna Amina Dikko Radda wanda hotunan ta ne har ƙaryata labarin yake wato yana nuna wannan shafin shine sahihi mallakar Ameena Dikko Radda to amma Alkalanci bata sami wani tabbacin shafin mallakar Ameena bane duk da cewa akwai mutane sama da dubu goma sha huɗu dake bibiyar shafin. Mutane da dama a comment section sun aminta da cewa shafin sahihi ne.
Instagram:
Sai kuma Alkalanci ta garzaya zuwa Instagram inda kamar sauran shafukan akwai da dama dake ɗauke da sunan Ameena Dikko Radda to amma a Instagram akwai wanda ya tabbata na ƴar gidan gwamnan Katsina ce Ameena Dikko Radda ne.
Ta buɗe wannan shafin na Instagram a watan Agustan 2018 kuma tayi verifying ɗinsa a shekarar 2025.

Haka zalika da muka duba shafin Instagram na matar gwamna Radda mai suna Zulaihat Abdullahi Dikko wacce ita ce mahaifiyar Ameena Alkalanci ta ga cewa tana bin shafin Ameena Dikko Radda.

Sannan mutane da dama sun tabbatar da cewa tana gudanar da Instagram live lokaci zuwa lokaci.
Sakamakon bincike:
Bisa samun waɗannan hujjoji da suka tabbatar da cewa Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa iƙirarin gwamnatin Katsina na cewa bata da wani shafin sada zumunta kwata-kwata ƙarya ne.
