BindiddigiCirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su...

Cirani: Shin Tarayyar Turai ta amince ‘yan Afrika su tsallaka ta Libya ba tare da Biza ba?

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa bayanan shafin majalisar dokokin kungiyar tarayyar turai da kuma bayanai da alkaluma dake nuna yadda EU ke daukar tsauraran matakan hana ‘yan cirani ko bakin haure tsallakawa zuwa turai ba bisa ka’ida ta wasu kasashen Afrika ya sa Alkalanci yanke hukuncin cewa wancan ikirari karya ne.

Duk da cewa kasashen turai na nuna damuwa tare da daukar matakan rage shigar bakin haure, ‘yan cirani dake tsallakawa ba tare da ka’ida ba wasu na yada ikirarai da labaran karya, tare da kwadaitar da matasa tsallakawa zuwa Turai.

Ikirari:
Wani shafin sada zumunta na Tiktok mai suna @zahaba__international (mista_aliyu) ya wallafa wani bidiyo inda yake ikirarin cewa;
“Kamar yadda kuka sani Turai ta ce a budewa ‘yan Afrika hanya masu sha’awar zuwa Turai ta Libya a bude musu hanya a daina kama su, an tura na daya ya tafi an tura na biyu ya tafi muna jiran na uku ya tafi…”
Ya kara wallafa wani makamancin wannan ma.
Bincike:
Kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta ci karo da bayanan tarayyar turai da ke nuna yadda kungiyar tarayyar Turai wato EU ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana ‘yan cirani da bakin haure, haurawa kasashen turai ba bisa ka’ida ba ta Libya.
Cikin bayanin Shugabar kungiyar tarayyar turai Ursula von de Leyen ta tabbatar da kokari da kudurin tarayyar turai na dakile tururuwar ‘yan ci rani, bakin haure wadanda ke shiga kasashen turai ba bisa ka’ida ba.
Tarayyar turai dai na taimakawa kasar Libya da makudan kudade da kayan aiki don dakile masu haurawa zuwa turai ba bisa ka’ida ba.
Dubban mutane ne ke rasa ransu yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa turai ba bisa ka’ida ba a cewar kwamitin IOM.
Baya ga yarjejeniya tsakanin EU da Libya kan ‘yan ci rani da bakin haure, kungiyar ta EU tana da fahimta da kuma yarjejeniya da kasashen Tunisia, Morocco, Senegal da Mauritania domin dakile masu zuwa turai ba bisa ka’ida ba.
Tarayyar turai dai ta ware kudi domin baiwa hukumomin kasar Mauritania da suka kai Euro miliyan dari biyu da goma €210m a shekarar 2024 domin dakile haurawar bakin haure da ‘yan cirani zuwa turai ba tare da ka’ida ba.
Har ila yau bayanin da aka wallafa a shafin majalisar dokokin tarayyar turai ya nuna cewa a watan Maris din wannan shekarar ta 2025 kungiyar ta EU ta gabatar da kudurin ganin an maida duk wani wanda ya shiga kasar turai ba bisa ka’ida ba da gaggawa. Cikin kudurin akwai ganin cewa an dauki matakin ganin cewa duk wani bakin haure bai gudu ba yayin da ake kokarin maida shi kasarsa ta asali, sannan kuma ga wadanda zasu iya fuskantar barazar tsaro a kasashen su za’a tsare su na tsawon watanni 24.
Kasar Libya dai tayi kaurin suna wajen safarar mutane zuwa turai, sanya mutane a gidajen yari sai an biya kudin fansa.
Majalisar dinkin duniya ta sha nuna damuwa kan yadda ake take hakkin mutane a Libya.
Sakamakon bincike:
Bisa bayanai da alkaluman da kafar tantance labarai ta Alkalanci ta samu na yadda tarayyar turai ke baiwa kasashen Libya, Morocco, Senegal Mauritania, Tunisia da masu kaura, zuwa cirani da tsallakawa zuwa turai ba bisa ka’ida ba ke bi. Sannan bayanan dake nuna yadda hukumomin tarayyar turai ke kara daukar tsauraran matakan hana ‘yan ci rani ko bakin haure shiga kasashen turai. Haka zalika babu wani gidan jarida sahihi daya rawaito cewa EU ta bude iyakarta ga ‘yan Afrika su shiga ta Libya wannan ya sanya Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari dake bidiyon karya ne.
Bayanin Edita: an sauya kudin da tarayyar turai ke baiwa Mauritania daga €12.5m zuwa miliyan €210 bayan samun takardar yarjejeniya tsakanin EU da kasar ta Mauritania a shekarar 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa wani labari tare da hotuna wanda ya yadu matuka da...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da suka bayyana cewa ‘yan Najeriya sunyi asarar makudan kudade yayin...

Shin Nijar ta rabu da Faransanci?

Tun bayan labarin amincewa da kuma ayyana Hausa a matsayin harshen kasa mutane ke ta wallafa labarin cewa Nijar...

Labaran ƙarya ne ke haddasa ƙiyayya tsakanin ‘yan kudu da ‘yan arewa

Shekara da shekaru dai ana samun rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar arewacin Najeriya a kudancin kasar. Abubuwan da suka...

Labaran karya daga Burkina Faso na cigaba da yaduwa a Najeriya

  Da dama daga ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta na cin karo da labarai kala-kala dangane da...

Najeriya-Saudiyya sun karyata labarin cewa za’a hana ‘yan kasar bizar shiga Saudiyya

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta karyata ikirarin karya da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wanda ke cewa...

Karanta wannan

Mutum uku ne suka mutu a hadarin hanyar Abuja zuwa Lokoja ba sama da mutane 100 ba

  Ikirari: Wani shafin Facebook mai suna Karaduwa post ya wallafa...

CBEX: Yadda zaku gane Idan kamfanin sanya hannun jari na da rijista

A ‘yan kwanakin nan an ga wasu rahotanni da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar