Akwai dai iƙirarai da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta da ke cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya mutu. Iƙirarin da ya fara da harshen turancin inda aka yi amfani da kalaman “Trump is Dead.”
Iƙiraran sun wallafa bidiyo da hotunan da ba a tabbatar da sahihancin su ba.
Bidiyoyin, hotuna da rubutattun maganganu ya ƙara rura wutar maganganun, sai dai babu wata hujja ko wata sahihiyar kafar yaɗa labarai da ta rawaito ko ta tabbatar da cewa Trump ya mutu.
Gidan jaridar EconomicTimes a wani rahoto ta danganta barkewar iƙiraran da jita-jitar da rahoton rashin lafiyar jijiyoyi da Trump ya kamu wanda aka sanar a watannin baya wanda likitan sa Dr. Sean P. Barbabella ya ce babu wata damuwa da yawa kan cutar ta shugaba Trump.
An kuma ji mataimakin shugaban na Amurka JD Vance a wata hira da yayi kafar yada labarai ta USA Today na cewa a shirye yake ya gaji Trump Idan wata mai afkuwa ta afku.
Haka zalika, wasu na zargin wani mai wasan barkwanci mai suna Simpsons ne ya yi hasashen cewa shugaba Trump zai mutu a shekarar 2025, to amma babu wata shaida dake cewa yayi wannan hasashe. To amma ana tunanin masu son shi ne suka samar da wannan bidiyo na ikirarin mutuwar shugaba Trump. Tuni dai kungiyar Simpsons ta karyata yin hasashen ko samar da bidiyon.
Sakamakon bincike:
Bisa rashin samun wata sahihiyar majiya ko shaidar cewa shugaban na Afrika ya rasu yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyo da hotunan da ake yaɗawa ƙarya ne.
