BindiddigiBayani kan raɗe-raɗin mutuwar shugaban Amurka Donald Trump

Bayani kan raɗe-raɗin mutuwar shugaban Amurka Donald Trump

-

Akwai dai iƙirarai da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta  da ke cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya mutu. Iƙirarin da ya fara da harshen turancin inda aka yi amfani da kalaman “Trump is Dead.”
Iƙiraran sun wallafa bidiyo da hotunan da ba a tabbatar da sahihancin su ba.
Bidiyoyin, hotuna da rubutattun maganganu  ya ƙara rura wutar maganganun, sai dai babu wata hujja ko wata sahihiyar kafar yaɗa labarai da ta rawaito ko ta tabbatar da cewa Trump ya mutu.
Gidan jaridar EconomicTimes a wani rahoto ta danganta barkewar iƙiraran da jita-jitar da rahoton rashin lafiyar jijiyoyi da Trump ya kamu wanda aka sanar a watannin baya wanda likitan sa Dr. Sean P. Barbabella ya ce babu wata damuwa da yawa kan cutar ta shugaba Trump.
An kuma ji mataimakin shugaban na Amurka JD Vance a wata hira da yayi kafar yada labarai ta USA Today na cewa a shirye yake ya gaji Trump Idan wata mai afkuwa ta afku.
Haka zalika, wasu na zargin wani mai wasan barkwanci mai suna Simpsons ne ya yi hasashen cewa shugaba Trump zai mutu a shekarar 2025, to amma babu wata shaida dake cewa yayi wannan hasashe. To amma ana tunanin masu son shi ne suka samar da wannan bidiyo na ikirarin mutuwar shugaba Trump. Tuni dai kungiyar Simpsons ta karyata yin hasashen ko samar da bidiyon.
Sakamakon bincike: 
Bisa rashin samun wata sahihiyar majiya ko shaidar cewa shugaban na Afrika ya rasu yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa bidiyo da hotunan da ake yaɗawa ƙarya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Karanta wannan

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar