A ranar asabar mai zuwa ne dai al’ummar ƙasar Kamaru zasu je runfunan zaɓe domin zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaban ƙasar mai ci Paul Biya na neman a kara zaɓen sa. Duk da cewa ‘yar sa a kwanakin baya ta yi kira ga ‘yan kasar da kada su zabi mahaifin nata.
Ga wasu alƙaluma dangane da zaɓen wanda muka samo daga hukumar zaɓen ƙasar ta Kamaru.
Shugabanni nawa aka taba yi tun bayan samun yancin kai?
Tun samun ƴancin kai a shekarar 1960 shugabanni biyu kacal ne sukayi mulkin shugabancin ƙasar.
Ahmadou Ahidjo wanda ya mulki ƙasar daga 1960 zuwa 1984 wato yayi shekaru 24 yana mulkar Kamaru.
Paul Biya ya fara mulki daga shekarar 1984 zuwa yanzu.
Yawan masu kada kuri’a
Ƴan ƙasar miliyan 8 da dubu ɗari biyu (8.2m) ne suka yi rijistar zaɓe. Kashi hamsin da hudu (54%) maza ne. Mata na da kashi arba’in da shida ((46%)
‘Yan takara nawa ne?
Akwai ƴan takara goma dake neman kujerar shugaban ƙasar ta Kamaru ciki har da shugaba mai ci Paul Biya mai shekaru 92.
Sai kuma wani matashi Hiram Samuel Iyodi mai shekaru 38.
Akwai kuma Issa Tchiroma Bakary da haɗakar wasu jam’iyyun adawa suka fitar wanda ya fito daga Garoua dake arewacin Kamaru. Ya kasance tsohon mai magana da yawan gwamnatin ƙasar.
Bello Bouba Maigari tsohon ministan yawan buɗe ido na ƙasar ta Kamaru.
Akwai kuma mace tilo dake naman takarar zama shugabar Kamaru.
