Fayyace abubuwaAbinda ya kamata ku sani dangane da zaɓen shugaban...

Abinda ya kamata ku sani dangane da zaɓen shugaban kasar Kamaru

-

A ranar asabar mai zuwa ne dai al’ummar ƙasar Kamaru zasu je runfunan zaɓe domin zaɓen shugaban ƙasa.

Shugaban ƙasar mai ci Paul Biya na neman a kara zaɓen sa. Duk da cewa ‘yar sa a kwanakin baya ta yi kira ga ‘yan kasar da kada su zabi mahaifin nata.
Ga wasu alƙaluma dangane da zaɓen wanda muka samo daga hukumar zaɓen ƙasar ta Kamaru.
Shugabanni nawa aka taba yi tun bayan samun yancin kai?
 
Tun samun ƴancin kai a shekarar 1960 shugabanni biyu kacal ne sukayi mulkin shugabancin ƙasar.
Ahmadou Ahidjo wanda ya mulki ƙasar daga 1960 zuwa 1984 wato yayi shekaru 24 yana mulkar Kamaru.
Paul Biya ya fara mulki daga shekarar 1984 zuwa yanzu.
Yawan masu kada kuri’a 
Ƴan ƙasar miliyan 8 da dubu ɗari biyu (8.2m)  ne suka yi rijistar zaɓe. Kashi hamsin da hudu (54%) maza ne. Mata na da kashi arba’in da shida ((46%)
Yan takara nawa ne?
Akwai ƴan takara goma dake neman kujerar shugaban ƙasar ta Kamaru ciki har da shugaba mai ci Paul Biya mai shekaru 92.
Sai kuma wani matashi Hiram Samuel Iyodi mai shekaru 38.
Akwai kuma Issa Tchiroma Bakary da haɗakar wasu jam’iyyun adawa suka fitar wanda ya fito daga Garoua dake arewacin Kamaru. Ya kasance tsohon mai magana da yawan gwamnatin ƙasar.
Bello Bouba Maigari tsohon ministan yawan buɗe ido na ƙasar ta Kamaru.
Akwai kuma mace tilo dake naman takarar zama shugabar Kamaru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Me yasa Amurka ta kai hari Sokoto?

Kasar Amurka ta takaddamar da hare-hare a wasu yankuna a arewacin Najeriya. Yanku nan sun hada da Arewa maso...

Duk da Iƙirarin gwamnatin Katsina Ameena Dikko Radda na da shafin Instagram tun 2018

Akwai wani hoto daya yaɗu matuƙa game da yar gwamnan jahar Katsina mai suna Amina dikko Radda inda aka...

Abunda ya kamata ku sani dangane da makamin BGM-109 Tomahawk

A ranar juma'a ne dai aka wayi gari da labarin yadda Amurka ta kai harin makami mai linzami da...

Bincike: Bidiyon Ali Baba Fagge da ke yawo a TikTok na zagin matar Ganduje haɗin AI ne

Iƙirari: A makon da ya gabata, wani bidiyo ya fara yawo sosai a kafar sada zumunta ta TikTok, wanda...

Karanta wannan

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar