Akwai wani bidiyo a kafar sada zumunta ta Tiktok inda wani shafi mai suna NajbelNursinghome ya wallafa inda aka sanya Illar Shan ruwan roba da na leda. An dai ji wanda ke magana a bidiyon yana cewa. “Ba ruwan bane yake da illa robar ce ko ledar ce… Sau hudu wadanda Ke da wannan robobi a jikinsu na iya samun heart attack. A yanzu dai roba da leda muke sha...”
Bincike:
Kafar tantance labarai bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano wani bincike na cibiyar lafiya ta Amurka NIH wacce ta tabbatar da samuwar wadannan kwayoyin roba da ke shiga ruwan da ke cikin roba ko leda. Binciken masanan ya nuna yadda aka sami kwayoyin roba a jini, huhu da wasu sassan na haihuwa.
To amma cibiyoyin binciken kansa sun musanta cewa shan ruwan roba ko leda da rana ta buga ko kuma yayi zafi a cikin mota na haddasa cutar kansa. Cibiyoyin sun tabbatar da samun kwayoyin roba a cikin irin wadannan ruwa, amma sunce ya zuwa yanzu babu wani bincike daya tabbatar da cewa shan ruwan roba na haddasa cutar kansa.
A Najeriya
Idan mun dawo Najeriya kuwa binciken masana lafiya da aka wallafa a kundin binciken magunguna da lafiya wato journal of Medicine and Healthcare, wanda Abubakar Mustapha Danraka da wasu suka yi kan ruwan roba dana leda ya fito da bayanai da dama.
Binciken da aka buga a kundin bincike.
Binciken ya tabbatar da cewa da dama daga cikin ruwan roba da ake siyarwa a Abuja babban birnin Najeriya cikin wasu an sami kwayoyin karfe wato metals da yawan su ya wuce ƙimar da WHO da hukumar kula da abinci da magunguna NAFDA suka amince da su don mutane su sha ba.
Sakamakon binciken da aka buga a kundin bincike.
Binciken da suka yi kan ruwan Leda ya nuna cewa mafi yawan waɗanda ake siyarwa a Abuja sun fa ɗi gwajin physiocochemical, kuma basu da inganci sannan basu cika sharruɗan fara buga ruwan sha da kuma lokacin da zai lalace wato expire ba. Sanna kashi 46 na ruwan ledar na da abinda ake kira Nickel yayin da kuma suke da kashi 40 na cadmium wanda ya haura abinda WHO ta kayyade.
Sakamakon bincike kan ruwan leda a Abuja.
Sakamakon bincike:
Bisa la’akari da waɗannan alkaluma da bincike wanda ya tabbatar da samuwar ƙwayoyin roba a cikin ruwan roba, musamman wanda rana ta buga.
Masana a sassan duniya dai sun bayyana cewa ya zuwa yanzu babu inda aka sami sakamakon cewa suna haddasa wata rashin lafiya misali heart attack da akai ikirari a wancan bidiyon.
wannan yasa kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa ruwan roba baya haddasa cutar da akai ikirari. Wanda za’a iya cewa a Najeriya ba robar bace matsala ruwan ne matsala.