BindiddigiShin Cin Nama Iftila’i ne Ga Lafiyar Mutane?

Shin Cin Nama Iftila’i ne Ga Lafiyar Mutane?

-

Hukumomi lafiya na duniya dai sun bayyana yawan cin ko cin jan nama da yawa da cewa na iya janyo wasu cututtuka. To sai dai basu bayyana naman kaza a ciki ba.

Akwai wani shafin kafar sada zumunta ta Tiktok mai suna @najbelnursinghome ya wallafa wani bidiyo mai tsawon mintuna shida inda yayi ikirari da dama duk dangane da cin nama.

Hoton bidiyon ikirarin dake yaduwa
Ga dai wasu daga cikin ikirarin dake bidiyon;
  1. Ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta fitar da ƙididdigar cewa kashi 75 har da dingo 6 na cututtuka da ake samu a abinci yana da alaka da cin nama.
  2. Sannan  kuma cibiyar kula da lafiya ta duniya ta fito ta fadi cewa a duk cikin mutum hudu mutum daya ya fuskanci babbar rashin lafiya a dalilin cin nama shine muke cewa food poisoning.
  3. Su kuma CDC sun fito sun fada cewa patrogyne da ake samu a nama kala uku ne, gaggan cuta da ake samu a cikin nama kala uku ne, akwai wanda muke cewa salmonella ita ce ake cewa tyP kashi 43 na cututtukan da ake samu a nama salmonella ce…. Kaga kenan mun gano inda ake samun typhoid.
  4. Hukumar lafiya ta duniya tace kashi 51 na masu cin nama anyi ittifakin cewa rabinsu kashi 51 cikin dari na iya samun hawan jini.
  5. Center for disease control  CDC cewa tayi cin nama a Najeriya anyi ittifakin yana da kyakkyawar alaka da kansa da ake samu ta dubura.
  6. Daga inda zaka ci fiye da fiffike guda na kaza gaskiya bansan me kake ci ba. Daga inda ka tauna na ka hadiye to ka tauna da bakinka kana hadiyewa to masifa ta fara a jikinka.

Bincike:

Binciken kafar tantance labarai, bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta binciki wadannan ikirari daya bayan daya.

1. Ko kashi 75.6 na rashin lafiya da ake samu ta abinci a Najeriya na da alaka da cin nama?

Da farko dai hukumar kididdiga ta kasa wato NBS ba ita ce hukumar lafiya ta Najeriya ba kuma cikin kididdigar da hukumar take fitarwa babu harkar lafiya a ciki.
A iya bincike dai hukumomin lafiya dai basu bayyana wancan ikirari na cewa kashi 75.6 na rashin lafiya da ake samu ta abinci na da alaka da cin nama ba.
To sai dai sun bayyana cewa kashi saba’in da wani abu na sabbin cututtuka da ake samu na da alaka da dabbobi wato zoonotic diseases a turance. Wanda ba wai dole sai anci naman dabbar ba takan yada cutar.
Haka zalika hukumomin lafiyar sun nuna damuwa kan rashin tsaftar mahautu a kasar wanda suka ce yana kara ta’azzara yaduwar cututtuka.
Wanda yasa Alkalanci bayyana wannan ikirari a matsayin na yaudarar tare da kawar da hankalin mutane.

2. Rabin food poisoning daga nama ne?

Binciken hukumar hana yaduwar cututtuka ta Amurka CDC ya bayyana abincin da ke haddasa matsalar food poisoning; cikin wadannan abinci dai ta nuna rashin barin abinci ya dahu sosai, cin danyen kwai, danyar fulawa, Shan madara ita kadai.
Ita kuma cibiyar lafiya ta NIH ta bayyana cewa cin danyen nama Ko wanda bai dahu sosai ba na iya haddasa food poisoning. Babu dai alkaluman kashin mutanen dake fama da wannan matsala. Binciken ya nuna cewa ba naman ne ke haddasa matsalar ta food poisoning din ba face rashin dafa shi da kyau ko cinsa danye ko kuma rashin tsafta.
Bisa wannan baya yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.

3. Nama na haddasa zazzabin typhoid?

Binciken Alkalanci dai ya gano cewa iya naman alade ne kadai yake dauke da kwayar cutar dake haddasa cutar typhoid. Wanda binciken dake kasa ya tabbatar da cewa cin naman alade na haddasa cutar typhoid.
Bisa lura da binciken masana da ya nuna cewa cikin nama, naman Alade ne ke dauke da kwayar cutar da ke haddasa typhoid za’a iya cewa akwai kamshin gaskiya.
Cutar Suga wato diabetes.
To amma bincike ya tabbatar da cewa yawan cin naman Saniya, Akuya da Alade na iya haifar da cutar 2 diabetes.
Kasancewar yawan cin jan nama na iya haddasa 2 diabetes Alkalanci ya yanke hukuncin cewa akwai kamshin gaskiya.

4. Ina gaskiyar  kashi 51 cikin dari na masu cin nama na iya samun hawan jini.

Binciken cibiyar lafiya ta NIH ya tabbatar da cewa yawancin naman Saniya, Akuya da Alade sosai na iya haddasa samun hawan jini.
Babu wata hukuma da ta fitar da adadi ko alkaluman da ya bayyana.
Naman kaza da sauran tsuntsaye basa cikin wannan.
Wannan ikirari shima akwai kamshin gaskiya duk da cewa akwai inda yake karya.

5. Alakar nama da kansa.

Binciken hukumar lafiya ta duniya WHO yace yawan cin jan nama da naman da aka sarrafa na iya haddasa cutar kansar mafitsara wato prostrate cancer.
Ita ma cibiyar binciken kansa ta Amurka AICR ta ce jan nama da naman alade sune ke haddasa kansar to amma fa cikin naman dai banda naman kaza, da kifi.
Akwai kamshin gaskiya.

6. Fiffiken kaza kadai ya kamata mutum yaci a sati?

Binciken cibiyar NHS ta Burtaniya ya tabbatar da cewa ana son mutum yaci nama akalla nauyin ounce 18 a sati. Domin hukumar ta bayyana cewa nama na dauke da sinadarai masu amfani a jikin mutum da suka hada da; iron, zinc B Vitamins.
Alkalanci ya yanke hukuncin cewa wannan ikirari na cin fiffiken kaza a safi kadai a matsayin karya ne.
Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar