Tun bayan da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ziyarci kasar Faransa akwai dai ikirari da labarai dake yaduwa wasu akwai kamshin gaskiya wasu kuma na karya.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna Lailu Hassan Moh’d ya wallafa wani bidiyo da a cikin bidiyo wani ke ikirarin cewa zuwan da shugaba Tinubu yayi zuwa Faransa ya sanya hannu kan yarjejeniya da Faransa na amincewa Faransa ta haki ma’adanan kasa a arewacin Najeriya.
“Babban hadari a gabanmu in ba addu’a ba abinda zai tsallakar damu last week din nan da wanna mutumin Bola ya ziyarci Faransa ya gana da shugaban Faransa sunyi yarjejeniya cewa Najeriya zasu bawa Faransa arewacin Najeriya zasu zo su debi ma’adanai karkashin kasa.”
Bincike:
Kafar bindiddigi da bincike ta Alkalanci ta gano cewa yayin ziyarar da shugaba Bola Tinubu yakai kasar Faransa ministan cigaban ma’adanan Najeriya ya rattaba hannu a madadin Najeriya kan batun bunkasa harkar ma’adana a Najeriya domin baiwa kasar damar raba kafa wajen hanyoyin shigar kudi.
Bayani daga ma’aikatar bunkasa harkar ma’adanai ya Najeriya tace yarjejeniyar ta kunshi batun hadin gwiwa wajen horaswa wato training, bincike wato research, da kuma musayar dalibai domin karin ilimi. Sannan yarjejeniya zata maida hankali kan yadda za’a sanya duk kamfanonin hakar ma’adanan kasa su kula da muhalli da rage amfani da injunan da suke gurbata muhalli.
Haka zalika yarjejeniya ta kunshi hadin gwiwa wajen sarrafa ma’adanai tare da tabbatar da cewa an kula da gururuwan dake kusa da guraren hakar ma’adanai kamar yadda yake a fadin duniya.
Ana kuma sa ran dawo da aiki a rijiyoyin ma’adanai dubu biyu da aka daina amfani dasu a sassana Najeriya.
Sakamakon Bincike:
Duk da cewa Najeriya da Faransa sun rattaba hannu kan batun ma’adanai to sai dai babu wani guri da aka bayyana cewa an baiwa kasar Faransa damar dibar ma’adanan kasa daga arewacin Najeriya kamar yadda mai ikirari yayi a wancan bidiyo. Kasancewar babu inda aka sami irin wannan bayani a rubuce ko a faifan sauti ko bidiyo dake nuna cewa an baiwa Faransa izinin dibar ma’adanai a arewacin Najeriya yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa wannan ikirari karya ne.