Tun bayan juyin mulkin soji a kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar kasashen uku suka sami takun saka da kungiyar ECOWAS inda suka bayyana aniyar ficewa tare da hada wata kungiyar mai suna AES. Wannan abu yazo da labaran karya da ake yadawa a kafafen sada zamunta kan kasashen dama kungiyar ta ECOWAS.
Batu:
Wani shafin kafar sada zumunta ta Tiktok mai suna @bashthausa ya wallafa wani rubutu dake ikirarin cewa; “ECOWAS ta amince da Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikinta.”
Rubuta ya kara da cewa ficewar ta kasashen zai fara daga watan Janairun shekarar 2025.
Bincike:
Binciken kafar bindiddigi ta Alkalanci ya sami sanarwar tare da saurarar bayanin bayan taron na shugabannin kasashen ECOWAS da aka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya inda shugaban ECOWAS Oumar Tourey ya sanar da kara wa’adin amincewa da ficewar kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar zuwa wata shida daga 29 ga watan Janairun 2025, domin baiwa kasashen damar ganin sun janye matakin ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.
Sanarwar ta bayyana cewa ranar 29 ga watan Janairun itace ranar ficewa a hukumance amma an dage ranar karshe ta zama ko ficewar kasashen zuwa 29 ga watan Yuli 2025, ECOWAS dai zatayi amfani da wannan lokaci domin ganin an sulhunta tsakanin kasashen da ECOWAS.
Kasashen na Burkina Faso, Mali da Nijar dai sunce babu jada baya kan ficewa daga ECOWAS amma yan kasashe mambobin ECOWAS zasu iya shiga kasashen ba tare da visa ba kamar yadda yake a yanzu.
Sakamakon Bincike:
Bisa sauraron jawabin shugaban kungiyar ECOWAS da umar kafar Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin akwai kamshin gaskiya.