BindiddigiIna Gaskiyar cewa Asiya Sulaiman Ibrahim Itace Mace Ta...

Ina Gaskiyar cewa Asiya Sulaiman Ibrahim Itace Mace Ta Farko Data Kammala Karatun Digiri A Yankin Falgore?

-

Garin Falgoren Daji dake karamar hukumar Doguwa gari ne dake bakin dajin daya hada jihar Kano da Bauchi kuma ya hade da dajin Yankari. Gari ne dake da kasuwa inda ake siye da siyarwar kayan noma da dabbobi.

Batu:

Akwai wani ikirari da wani shafin Facebook mai suna RFI Hausa ya wallafa wani bidiyo mai tsawon mintuna biyu tare da rubuta cewa wata mata dake bidiyon itace mace ta farko data kammala karatun digiri a yankin Falgore karamar hukumar Doguwa dake jihar Kano.
Mace ta farko da ta kammala karatun digiri a yankin Falgore dake karamar hukumar Doguwa a jihar Kanon Najeriya.”
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa.

Bincike:

Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta fara bincika kafin ita wannan mata a bidiyo da akai ikirari akwai mace ‘yar wannan gari ta Falgore data kammala karatun digiri? Alkalanci mun gano cewa akwai mata da suka kai akalla hudu da suke yan asalin wannan gari na Falgore ne kuma sun kammala karatun digiri shekaru kafin ita wacce aka wallafa a bidiyon wacce ko hidimar kasa wato NYSC ma batayi ba.
Mun tuntubi wani dan asalin wannan gari na Falgore kuma ma’aikaci a jami’ar ABU mai suna  Nuraddeen Adam Iliyasu wanda yace; “Akwai mata ‘yan asalin garin Falgore da suka kammala jami’a. Ina farin ciki cewa ita wannan mata mai suna Asiya ‘yar garin namu na Falgore  ta kammala digiri amma batun cewa ita ta farko bai taso ba.”
Ga sunayen wasu daga cikin matan da ‘yan asalin wannan gari na Falgore ne, kuma sun kammala  karatun digiri.
  1.  Hadiza Ibrahim BSc. Adult Education 2018
  2.  Halima Ibrahim Yusuf BSc. Nursing (BUK)2021
  3. Bushira Garba Abdu B.Ed (ABU)2023
  4. Hajara Ibrahim BSc. English (BUK)2020
Ya kara da cewa, “dukkan su Idan anzo karbar tallafin karatu wato scholarship takardun shaidar gari na asali dama karamar hukuma duk na Falgore da karamar hukumar Doguwa ne.”
A ikirarin ance yankin Falgore wanda hakan ke nufin garuruwan dake kusa da Falgore inda Nuraddeen ya kara da cewa; “Yankin Falgore suna nufin Idan ka hauro daga daji kenan, to ya zasuyi da mata da yawa da suka kammala digiri ‘yan asalin garin Burji?”

Sakamakon Bincike:

Bisa samun bayani daga ‘yan wannan gari tare da tabbatar da cewa wadancan sunaye ‘yan asalin wancan gari na Falgore ne, yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin RFI Hausa na cewa Asiya itace mace ta farko data kammala digiri daga yankin Falgore karya ne.

Labarai masu alaka: 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar