Fayyace abubuwaMatakan Kare Kai Daga Masu Cire Kudi Daga Asusun...

Matakan Kare Kai Daga Masu Cire Kudi Daga Asusun Ajiya

-

Wasu garuruwa da birane a Najeriya na fama da karancin takardun Naira wanda ya sanya wasu suka koma yin harkar cinikayya da tura kudi ta yanar gizo wato digital.
Kasancewar dama kafin wannan lokaci wasu na zambatar mutane tare da kwashe musu kudade a asusun ajiyar su ta hanyar yaudara ko zamba.
Haka zalika suma masu sana’ar POS ko masu shaguna dake da na’urar ta POS basu tsira ba domin akwai masu amfani da wata fasaha ko dai ta tura kudi aga kamar ya shigo ko kuma aga cewa an sami approval na cire kudi amma basu shiga asusun ba.
Ga wasu matakan da zaku iya dauka don kare yiwuwar a damfareku ko a kwashe muku ‘yan canjin ku dake asusun ajiyar ku na banki.

Ga masu cirar kudi:

1. Idan kuna da kudi da yawa a asusun ajiyarku to ku kayyade yawan kudin da zaku iya cira da ATM ko wanda zaku iya turawa wato transfer a rana guda. Domin Idan kunyi haka koda an sami damar samun bayanan da za’a iya cirar kudi a asusun ajiyar iya yawan wanda kuka kayyade za’a iya cira, wanda kafin abun ya kai wani mataki kun kulle asusun ajiyar.
2. Kada ku baiwa wani lambar sirrin katin ku na ATM, kuma ku dinga kaffa-kaffa dashi. Sannan kada ku bari wani wanda ba ma’aikacin banki ba yace zai tayaku ko koya muku cirar kudi a ATM wanda watakila har zai danna muku lambobin sirrin katin. Akwai dai mutane da dama da suka fada tarkon ‘yan damfara dake zuwa kusa da injinan ATM don canza katin mutane bayan sun ga lambar sirri wato PIN.
3. Idan kunje cirar kudi ku kula sosai da na’urar ATM domin wasu lokuta wasu na sanya abubuwa a bakin na’urar daka iya nadar bayanan katin wanda bayan kun gama suyi amfani da bayanan wajen kwashe muku kudade. Da zarar baku aminta da naurar ATM ba to ku sanar da jami’an bankin ko kuma ku sauya wani. Idan kuwa ta POS zaku ciri, kuje inda kuka aminta da.
5. Ku tabbatar kuna samun alert ta hanyar text da kuma email domin tabbatar da kudi ya shiga ko ya fita. Wanda Idan kuka sami fitar kudi da baku sani ba, ku gaggauta sanar da bankinku domin su dauki mataki. Sannan kusan lambobin da zaku iya rufe asusunku duk lokacin da masu zamba suka fara cire muku kudade.

Ga Masu Sana’ar POS:

  1. Ku tabbata katin ATM din na dauke da bayanai da kowannen kati yake dashi wato rana da watan da zai daina aiki wato expiry date. Sannan ku kula da duk wani katin ATM da baku aminta dashi ba kada ai muku sakiyar da babu ruwa.
  2. Ku mallaki app na bankin da kuke amfani dashi domin duba fita da shigar kudade.

Labarai masu alaka:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya da suka shafi bangarorin biyu wato bangaren Sarki Aminu Ado...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan kiyashin kiristoci a Najeriya da kuma bayanin yiwuwar turo da...

Bidiyon Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto haɗin AI ne 

Bayan hukuncin da koto tayi na ɗaure Nnamdi Kanu bisa laifin ta'addanci, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta...

Rasha da Amurka ne kan gaba wajen yaɗa labaran ƙarya a yammacin Afirka cewar Fauziyya Kabir Tukur

Shekara da shekaru ƙasashen duniya kanyi amfani da yaɗa labarai wajen yaƙi da juna ko haddasa rikici a wasu...

ƙirƙirarrayir basirar AI wanne hali Najeriya ke ciki?

A cikin watan Satumba, 2025 aka samu wani shafi na caca ya ƙirƙiri bidiyo da hoton talla na ƙarya...

Ƙarya ne: Saudiyya bata cire ɗarikar Tijjaniyya daga cikin akidu da ke da alaka da musulunci ba

Wani shafin TikTok mai suna prince hassan ya wallafa labarin cewa hukumar Saudiyya ta cire Tijjaniyya cikin jerin akidun...

Karanta wannan

Labarin cewa Christopher Musa ya bai wa Aminu Ado Bayero wa’adin awa 24 ya je ya same shi, ƙarya ne

Tun bayan tababar sarautar Kano ake samun labaran karya...

Labaran ƙarya da ake yadawa kan kalaman Trump a shafukan Facebook

Tun bayan iƙirarin shugaban Amurka Donald Trump na kisan...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar