Suma malaman addini basu tsira ba wajen yada labaran karya akan su.
Batu:
Wani shafin Facebook mai suna Damagaram Post ya wallafa wani labari cewa Farfesa Ibrahim Maqari na Najeriya ya zama dan Najeriya na farko da yafi kowa ilimin hadisi a Afrika.
“Ɗan Najeriya ya zama mutum na farko da yafi kowa ilimin Hadisi a Afrika.
An zaɓi Farfesa Sheikh Prof. Ibrahim Maqari daga Najeriya a matsayin wanda yafi kowa ilimin sanin Hadisan MANZON ALLAH SAW a kaf nahiyar Afrika. Barbara Jami’ar Musulunci ta farko wato Al’azahar dake ƙasar Masar ta ayyana babban limamin Najeriya Professor Ibrahim Maqari a matsayin wanda yafi kowa ilimin sanin Hadisan MANZON ALLAH SAW da Fiqhu.”

Bincike:
Kafar bindiddigi ta Alkalanci ta binciki wannan ikirari inda ta gano cewa an fara yada labarin a ranar 3 ga watan Disembar 2023, yayin da shi kuma hoton an fara amfani dashi a watan Fabrairun shekarar 2022.

Sannan kafar Alkalanci ta tuntubi kanin Farfesa Ibrahim Maqari mai sun Fuad Maqari kan wannan labari dake yaduwa a kafafen sada zumunta inda ya fara tuntubar Farfesa Maqari wanda ya bashi damar yin magana a madadin sa kan wannan batu.
Fuad ya bayyanawa Alkalanci cewa; “Malam bai zo kusa da wannan batu ba, domin idan ana magana ta hadisi a Najeriya ma akwai Shaikh Shariff Saleh, kuma malamin Farfesa Maqari ne.
A yanzu Malam Sahihul Bukhari, da Muwadda Malik kawai yake karantarwa ma a fannin hadisi domin yafi mayar da hankali ga ilimin Fiqhu.”
Ya kara da cewa; “Wannan dai labarin karya ne, kuma ba labari ne da duk wani mai ilimi zai kula dashi ba, daliban malam ma dariya kawai suke. Maganar jami’ar Azhar kuwa ai ita Azhar nada malamai irin su malam sosoi, kuma Morocco da Aljeriya duk suna da irin malam dama wadanda suka fishi ilimin hadisi.”
“Tabbas kwanaki Malam yaje Morocco karbar kyauta, wannan kyauta ba tashi bace, ya karba a madadin shaikh Shariff Saleh ne. Wani abu da mutane basu sani ba ko wannan taron ma bashi da alaka da ilimin hadisi.”
Sakamakon Bincike:
Kasancewar labarin dama sabun tashi akayi shekara guda bayan an fara yada shi kuma shi kansa Farfesa Maqari ta bakin kaninsa sun bayyana cewa babu wani abu makamancin haka daya faru tare da ayyana ikirarin a matsayin karya. Haka zalika babu wata kafar yada labarai sahihiya ta kowanne yare data yada irin wannan labari wanda yasa kafar bindiddigi ta Alkalanci ta yanke hukuncin cewa wannan labarin karya ne.