Labarun karya da na kawar da hankulan mutane dai na cigaba da yaduwa a kafafen sada zumunta musamman kan halin da ake ciki a yammacin Afrika da wasu yankunan Sahel.
Ikirari:
Wani matashi ya wallafa wani bidiyo mai tsawon minti daya da sakan arba’in (adana bayanai a NAN) da ku a shafinsa na TikTok mai suna @kebi.ne inda yake ikirarin cewa shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya zanta da shugaban Rasha Vladimir Putin inda ya bukaci Putin daya sa shugabannin kasashe Burkina Faso, Mali da Nijar su koma kungiyar ECOWAS.
“Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye ya tafka abin kunya ga kasashen mu na AES. Abunda ake ta tafka mahawara a kafafen sadarwa shine aikin da yayi na kiran shugaban Rasha Vladimir Putin akan ya bawa kasashe AES shawara kan su koma tsohuwar kungiyar nan ta ECOWAS…”
Hoton rubutun da aka wallafa dake cigaba da yaduwa
Bincike:
A binciken kafar bindiddigi ta Alkalanci ta samo bayanin tattaunarda shugabannin kasashen biyu na Senegal da Rasha sukayi a shafin gwamnatin kasar Rashar.
Rasha tace zantawar anyi tane kan yadda kasashen biyu zasu karfafa alaka ta kawance, tattalin arziki, kasuwanci, noma da fannin sufuri. Sanarwar ta kara da cewa shugaban Senegal ya bukaci samun sana’o’in Rasha a kasar sa domin cigaba. Inda shugaba Putin ya gayyaci shugaban Senegal zuwa Rasha inda ya amince.
Har ila yau shafin gwamnatin kasar Senegal shima ya wallafa bayanin tattaunawar inda yace anyi tane kan batun karfafa kawance da yadda za’a kawo karshen matsalar tsaro a yammacin Afrika.
Kafafen yada labarai na duniya duk sun rawaito labarin tattaunawar amma kan batun tsaro da tattalin arziki tare da gayyatar da Putin yawa shugaban na Senegal.
Sakamakon Bincike:
Binciken kafar Alkalanci dai bai sami guri daya da aka ambato cewa shugaban kasar Senegal ya bukaci Putin daya sanya baki kan kasashen AES su koma ECOWAS ba. Sannan babu wani gidan jarida ko daya da ya kawo irin wannan ikirari. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin karya ne.