Gidauniyar bankin UBA dai na daukar nauyin gasar rubutun insha’i wato essay competition, shekaru sama da goma, wanda yara ‘yan makaranta kan shiga.
Batu:
A tsakanin asabar 23 zuwa lahadi 24 ga watan Nuwamban shekarar 2024 ana ta yada hoton wata yarinyar mai suna Khadijah AbdulHameed wacce ake ikirarin taki yin masabaha da shugaban bankin UBA bayan tazo na biyu a gasar saboda addininta na musulunci bai bata dama ba.
Wani shafin Facebook mai suna Jaridar Arewa ya wallafa wannan labari a ranar lahadi 24/11/2024 a matsayin labarin daya faru a ranar. “ DA ƊUMI-ƊUMI: “Addini na ya hana hakan” Khadijah taƙi amincewa da musafaha da shugaban bankin UBA Sunanta Khadijah Abdulhamid, Husna daga makarantar Sakandaren Sweet Haven ta Jihar Kano, ta ki amincewa da musafaha da Oliver Alawuba, Shugaban Kamfanin UBA, a wajen gabatar da lambar yabo ta UBA Foundation Nigeria, inda ta ce Addininta ya hana hakan. Daga Usman Umar Katsina”
Wannan hoto dai na cigaba da yaduwa inda ake nuna cewa abun ya faru ne a wannan shekarar ta 2024.

Bincike:
Kafar bindiddigi Alkalanci ta bincika hoton inda ta samo cewa wannan hoto an fara yada shine a watan Nuwamban bara wato 2023 lokacin da Khadijah AbdulHameed tazo ta biyu a gasar gidauniyar UBA karo na goma sha uku. A gasar dai Khadija ta sami kyautar Naira miliyan Uku.
A wancan lokaci mutane da dama sun yada wannan hoto dauke da bayanin yadda taki yin musabahar.

Sakamakon Bincike:
Binciken kafar Alkalanci ta tabbatar da cewa tabbas hoton gaskiya kuma ya faru, kuma Khadijah ta wakilci makarantar ta Sweet Haven dake Kano, to amma ba a wannan shekarar ta 2024 ne ya faru ba. Don haka ikirarin ko labarin dake nuna a wannan shekara ta 2024 abun ya faru ba gaskiya bane.