Kwanaki sama da bakwai kenan jihohi arewa maso yamma bakwai, Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara, arewa maso gabashi guda shida Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sai jihohi biyu a arewa maso tsakiyar Najeriya jihohin Filato da Benue duk da cewa akwai sassa na jihohin Nasarawa da Kogi basu da wutar lantarki daga tashar bada wuta ta kasar wato national grid.
Hakan ne ya tilasta majalisar dokokin jihar Nasarawa kiran hukumar rarraba wuta ta AEDC ta gurfana a zauren majalisar don jin bahasi.
Jihohin Neja da Kwara kadai ne wannan matsala bata shafa ba.
Kafin wannan matsala da daukewar wutar ga jihohin arewa an sami rugujewar turakun wutar ta kasa wato national grids sau uku cikin sati guda. A ranar 19-10-2024 shafin national grid din @NationalGridNg ya wallafa cewa an sami daukewar wuta gaba daya Najeriya saboda rugujewar da yayi wanda shine na uku a kwanaki bakwai.
Hukumar samar tare da rarraba wutar lantarki ta TCN a ranar talata 22-10-2024 ta fitar da sanarwar cewa lalacewar layin samar da wuta na shiroro-Mando ne abinda yasa babu wuta a jihohin arewa 17.
Yayin da ake cigaba da samun rashin wutar lantarkin sai wani labari ya yadu a kafafen sada zumunta Ina ake ikirarin cewa wata shugaba a hukumar TCN Nafisat Asabe tace babu ranar dawo da wutar lantarki a Arewacin Najeriya.
Wannan labari ya yadu matuka a kafar sada zumunta ta Facebook dama wasu jaridu.
Misali wani mai suna Abdul-Hadee Isah lbraheem yace “Shugabar hukumar wutar lantarkin ta TCN na Nigeria Nafisat Asabe tace “Babu tabbacin ranar da wutar lantarki zata dawo gaba daya a Arewa, saboda matsalar tsaro dake hana aikin gyaran wutar”.
Irin Wadannan kalamai dai sun yadu matuka a shafukan sada zumunta.
Alkalanci ya tuntubi ofishin ita Nafisatu Ali wacce darakta ce a hukumar ta TCN inda bamu sami amsar ta fadi hakan Ko bata fada ba.
Bayan kwana guda da tuntubarta sai hukumar ta TCN ta hannun Darakta sashen hulda da jama’a Ndidi Mbah ta fitar da sanarwa dake musanta wancan zargi, inda sanarwar tace hukumar ta TCN tuni tana aiki da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro NSA don ganin an baiwa wadanda zasuyi aikin gyaran layin wutar tsaro yayin da suke aiki a inda aka lalata layin raba wuta na Shiroro-Mando.
Hukumar dai ta zargi ‘yan ta’adda da lalata layin wutar lantarkin da yake baiwa arewacin kasar.
Sannan sanarwar tace tuni tana aikin ganin ta samar da hanyar wucin gadi da za’a sami wuta a arewacin kasar ta layin raba wuta na 330kV ugwuaji-Apir.
To sai dai har ya zuwa yau 28-10-2024 ba’a sami wutar lantarkin ba wanda ya zuwa yanzu babu wani Wallafa da aka karayi kan wannan batu a shafin nasu na X.
An dai yada wannan wallafi daga shafin nasa sama da dari biyu.
Yan kasuwa da masana’antu nata kokawa kan wannan rashin wuta inda wasu suka bayyanawa gidajen jaridu irin asarar da sukayi da kuma wacce ka iya faruwa Idan wannan matsala ta kara daukar dogon lokaci.
Kungiyar dattawan arewa dai ta fitar da sanarwa inda take zargin cewa wannan rashin wuta a arewa hanya ce ta durkusar da yankin.
Yan awanni bayan wannan sanarwa fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar manema labari dake nuna damuwar shugaban kasa kan batun katsewar wutar ta arewa inda sanarwar tace tuni shugaban kasar ya gana tare da baiwa ministan wutar kasar da mai bashi shawara kan harkokin tsaro dasu gaggauta gani an bada tsaro don gyara layin wutar na Shiroro-Mando.
Ko a watan satumbar daya gabata yan kungiyar Boko Haram sun lalata layin wutar lantarki na Gombe-Damaturu-Maiduguri wanda yasa biranen Damaturu da Maiduguri cikin duhu na wani dan lokaci.
Tambayoyin da mutane da dama keyi shine bayan an gyara zai zama na karshe kenan da yan bindigar zasu lalata layin wutar ko kuwa?
Cikin sanarwar da fadar shugaban kasar dai ta fitar akwai kiran da yayi ga masu ruwa da tsaki da su bada hadin kai da gudummawa wajen kare kayan gwamnati daga masu lalata ko sata.
Labarai masu alaka: