Asusun bada lamuni na duniya wato IMF dai wani asusu ne mai mambobin kasashe 191 da aka samar don bada lamuni, tare da shawarwari kan tattalin arziki. Asusun mai shalkwata a birnin Washington DC na Amurka an samar dashi ne a shekarar 1944.
Yana da karfin bada bashin kudin daya kai dala tiriliyan daya ga mambobin asusun.
Najeriya dai ta zama mambar asusun na IMF a ranar 30 ga watan Maris din 1961.
Batu:
A ranar Juma’a 25 ga watan Oktoban 2024 ne dai kafafen yada labaran Najeriya dama wasu kasashe suka ruwaito asusun ya nesanta kansa daga ikirarin da akeyi na cewa shine ya baiwa shugaba Tinubu shawarar cire tallafin man fetur wanda ya janyo karin matsin rayuwa da tattalin arzikin ‘yan kasar.
Wannan yasa Alkalanci zai dubu wannan bayani daya fito daga asusun bada lamunin domin sanin shin ya abun yake?
Bindiddigi:
Tallafin mai dai a Najeriya ya samo asali ne daga shekarar 1977 a matsayin matakin wucin gadi lokacin da aka sami tashin farashin danyan mai a kasuwar duniya, tun daga waccen shekara ce dai gwamnatoci na soji dama na damakradiyya suka ci gaba da bayin kudin tallafi domin talakawan kasar sun sami mai da sauki. Musamman lokacin da farashin mai yayi tashin gwauron zabi tsakanin shakarar 2000 zuwa 2012.
A tsakani 2011 zuwa 2012 gwamnatin Goodluck Jonathan tayi kokarin cire tallafin mai to amma ta sami matsin lamba daga majalisar tarayyar kasar tare da zanga-zanga wanda ya tilasta gwamnati janye wannan kuduri.
Shekara da shekaru dai asusun na IMF na kokarin baiwa kasashen mambobi shawara kan tattalin arzikinsu tare da bada bashi ciki harda Najeriya.
Rahoton IMF dake shafinsa daya fitar a ranar 18 ga wantan Nuwamba, 2022, yayi kakkausar magana tare da bada shawara na bukatar cire tallafin mai na din-din-din. Zaku iya duba rahoton ta wannan link a
NAN.
Sannan a rahotanni guda biyu na IMF daya a fitar a
watan Fabrairun shekarar 2022 da 2021 a cikin rahotonnin ya shawarci Najeriya data cire tallafin man fetur tare da baiwa gwamnati shawara na samar da hanyar kare talakawa daga fadawa matsanancin hali.
A
cikin rahoton akwai inda asusun ke cewa tallafin man fetur abune da yake maida cigaban kasar baya.
Lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari dai an sha jin cewa an cire tallafin mai wato subsidy amma daga baya sai asusun IMF da banki duniya su kwarmata cewa tallafin man fetur din dai yana nan ana cigaba da biyanshi.
A watannin karshe na mulkin Buhari sai gwamnatin sa a kokarin cire tallafin baki daya taki sanya kudin tallafi a cikin kasafin kudin a shugaba Bola Tinubu zai gada wanda ya sanya shi sanar da yan kasar cewa tallafin man fetur dai an daina biya a ranar daya karbi mulki.
Wannan ne yasa mutane da dama suka dinga fadin cewa shine ya cire tallafin ba tsohon shugaban kasar ba Muhammadu Buhari.
Bindiddigi jaridu da dama Kan wannan batu wanda ya hada harda jaridar
Daily Trust ya gano tare da tabbatar da cewa gwamnatin baya ce ta cire tallafin man fetur din.
Kasancewar dama babu batun kudin tallafin man fetur a kasafin kudin watannin farko zuwa watan Yunin
2023 rahoton IMF daya fitar a watan Fabrairun 2023 bai ambaci batun tallafin bama kwata-kwata.
To sai dai baya ga dukkan wadancan shawarwari da asusun na IMF ya dinga baiwa Najeriya kan ta cire tallafin man fetur Sai kuma ranar 25 ga watan Oktoban 2024 aka ji Daraktan IMF mai kula da Afirka Abebe Aemro Sellasie na cewa batun cire tallafin man fetur na Najeriya batu ne na cikin gida kuma na siyar cikin gida wato Najeriya, yace “
bamu da wani shiri a Najeriya face rahoton da muke fitarwa kamar yadda mukayi da wasu kasashen SWANA, Asiya, Japan da UK, tare da bayyana ra’ayin mu ko tinaninmu kan abinda ya dace ayi da albarkatu ko dukiyar kasa. Dangane da Najeriya mun bada ra’ayi ne mai karfi kan yadda ake cigaba da biyan tallafi kan man fetur dama wasu abubuwa.” Ya kara da cewa
“wannan dai batune na cikin gida kuma na siyasa mai karfi da dole gwamnati ta dauka. Kuma muna na’am da wannan mataki domin zai taimaka wajen bude damarmakin samun cigaba…” Ga link din taron manema labaran a
nan.
Karshe:
A iya binciken da Alkalanci yayi bai samo inda asusun na IMF ya baiwa shugaba Tinubu shawarar cire tallafi ba domin kuwa kafin ma ya hau dama babu kasafin kudin biyan tallafi. Haka zalika Alkalanci ya gano ciwo babu inda asusun IMF ya fito karara yace bashi da hannu kan batun cire tallafin face ma dai nuna farin ciki da matakin.
Labarai masu alaka: