Shekara da shekaru dai hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA na kokawa kan matsalar shaye-shaye musamman tsakanin matasa.
Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya taba bayyana cewa shaye-shaye shine yake taimakawa wajen ta’azzara matsalar tsaro a sassan Najeriya.
Ikirari
A shafin X (Twitter) wani mai suna Imran Muhammad @imranmuhdz ya wallafa rubuta da bidiyo dake nuna mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Najeriya Sanata Lola Ashiru yayin magana a Zauren majalisar yayi ikirarin cewa sama da kashi saba’in na matasan Najeriya na ta’ammali da kwaya.
“Ba tare dayin rowar kalamai ba sama da kashi saba’in na matasan mu na ta’ammali da kwaya, kuma a cikin yar karamar zantawa a mazaba ta wannan batu yafi karfin NDLEA, NDLEA sun zama magen lami, basu da tasiri, sabida haka barin yaki da Shan miyagun a hannun NDLEA bazai kaimu gaci ba.”
Bincike
A shekarar 2018 hukumar kididdiga ta Najeriya tare da hadin gwiwar ofishin yaki da kwayoyi da laifuka na majalisar dinkin duniya da kuma tarayyar turai sun fitar da wani rahoto dangane da ta’ammali da kwaya a Najeriya inda rahoton ya nuna cewa yan Najeriya miliyan 14.3m suke ta’ammali da kwaya a kasar wato kashi 14.4%.
Haka zalika a shakarar 2021 hukumar NDLEA tace kashi arba’in na matasa tsakanin shekaru 18-35 na ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Wani rahoto na majalisar dinkin duniya ya kuma kara da cewa daga nan zuwa shakarar 2030 ana iya samun karin masu ta’ammali da kwayoyi zuwa miliyan 20.
Sakamako
Bayan Binciken alkaluma na yawan masu Shan miyagun kwayoyi a Najeriya dama yawan jama’ar kasar da ake kiyasta sama da miliyan dari biyu ya nuna cewa wannan ikirarin ba gaskiya bane wato false a turance.
The senator just said it to push his argument that another agency should be created to tackle drug related issues