Gabatarwa
Shekaru da dama dai yan Najeriya na ganin cewa kasar bata kan turbar dai-dai wato tana bukatar saiti ko ace gyara, musamman yadda ake fito da yadda aka sami wasu da suka rike shugabanci da almundahan tare da yin rub-da-ciki da kudaden yan kasar.
Wasu kasashe dai musamman a Asiya nada tsarin hukunci mai tsauri ga duk shugaban da aka samu da cin hanci Ko rashawa. Kasar Koriya ta arewa na cikin kasashen da mutane ke ganin cewa shugaban kasar baya wasa da batun doka da oda da kuma tabbatar da kasar ta sami cigaba da fannin mallakar makamai wanda ya hada da makamin kare dangi na nuclear.
Ikirari
Wani shafin Facebook mai suna Vanguard Hausa ya wallafa wani rubutu tare da hoton shugaban kasar Korea ta arewa inda rubutun ke cewa;
“Zan iya gyara Najeriya cikin shekara daya kacal. Kuma idan aka ba ni Nijeriya na yi masu mulkin mallaka, a cikin shekara daya zan mayar da su cikin rukunin manyan kasashen duniya, Cewar matashin Shugaban Kasar Koriya ta Arewa Kin Jong Un. Me za ku ce?”

Wannan rubutu ya sami yadawa wato shares sama da dari uku yayin da mutane da dama suka bayyana nasu ra’ayin.
Misali Yusuf Musa Numan yace “Ni nasan da hakan zai kasance tabbas zaka iya gyara Najeriya.”
A shafin X wato Twitter wata mai lakabin @Ameenatu_ itama ta wallafa irin wancan post inda yake cewa; “Zan iya gyara Najeriya cikin shekara daya kacal-Inji shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un.”

Mutane sama da dari biyu ne suka tofa albarkacin bakinsu yayin da mutane sama da dadi bakwai suka danna like.
Bincike
An taba wallafa makamancin wannan kalamai a shekarar 2018 wanda Binciken da kafar jarida ta ICIR tayi ya nuna cewa wani shafi mai yada labaran karya da farfaganda mai suna Aljazeera West Africa ce ta fara wallafa shi. Saboda rashin shaida za’a iya cewa wancan labarin na aka sabunta ya dawo domin cimma wata manufa.
Sakamakon Bincike
Bincike da alkalanci yayi ya nuna cewa wannan bayani karya ne kawai, wato false a turance.