Hukunci: Ƙarya ne
Ali Nuhu ya tabbatarwa Alkalanci cewa karya ne bai samar da asibiti mallakinsa a Abuja ba. Kuma binciken Alkalanci ya tabbatar da samun hoton da ake yadawa na kirkirarriyar basirar AI ne, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin da hotunan da ake yadawa cewa Ali Nuhu ya samar da cibiyar kula da lafiya dauke da sunan shi a Abuja karya ne.
Akwai dai wani labari da kuma hotuna dake matukar yaduwa a kafafen sada zumunta dake ikirarin cewa shahararren dan wasan kwaikwayo Ali Nuhu ya samar da cibiyar kula da lafiyar mutane wato Medical center a Abuja.
Hoton wanda aka rubuta Sarki Ali Nuhu Medical Center Abuja.
Akwai dai wannan shafin Tiktok din ((https://vm.tiktok.com/ZSShHhYGX/)) wanda yayi ikirarin cikin asibitin.

Akwai ma wannan ((https://vm.tiktok.com/ZSSrrG5t8/)
Sannan akwai shafuka da dama a Facebook da suka yada wannan labari. ((https://www.facebook.com/share/1Pyr534fdK/?mibextid=wwXIfr))
Dukkan shafukan dai na wallafa hoto da kuma rubutu kamar haka “ SARKI ALI NUHU MEDICAL CENTRE ABUJA.”

Bincike:
Kafar tantance labarai ta Alkalanci ta tuntubi Ali Nuhu kai tsaye inda ya bayyana cewa ba gaskiya bane domin shi bai bude wani asibiti ko cibiyar lafiya ba. “Tabbas na ga wani hoton da akayi da kirkirarriyar basirar AI da ake cewa asibiti na ne da na bude a Abuja.”
Haka zalika kafar Alkalanci ta sanya hoton kan manhajar duba hotunan da akayi da kirkirarriyar basirar AI inda manhajar ta tabbatar da cewa hoton hadin AI ne.
Ali Nuhu dai baya ga kasancewar sa gwarzon dan wasan kwaikwayo a yanzu haka shine shugaban hukumar harkokin fina-finai ta Najeriya wato Nigeria Film cooperation.
Sakamakon bincike:
Bisa bayani daga bakin Ali Nuhu inda ya musanta samar da asibiti mallakinsa a Abuja, da kuma tabbatar da samun cewa hoton da ake yadawa na kirkirarriyar basirar AI ne, wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin da hotunan da ake yadawa cewa Ali Nuhu ya samar da cibiyar kula da lafiya dauke da sunan shi a Abuja karya ne.
