Hukunci: Ƙarya ne
Bincike kan hoton dai ya tabbatar da cewa an kirkireshi ne ta amfani da AI kuma an yada bidiyo hoton a kasar India. Sannan gadar da aka sami ruftawar wani bangare na gada a Keffi ne kuma ba gaba daya ta rufta ba. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin gadar da aka kaddamar a Nasarawa ta rushe karya ne.
Wani shafin Facebook mai suna Kabiru Danladi Lawanti ya wallafa wani hotu inda yake ikirarin cewa “ An ce nan ₦10bn flyover ce ta rushe bayan sati uku da ƙaddamar fa ita a Nasarawa State. Biliyan goma fa.”

((https://www.facebook.com/share/p/199MbHZorJ/?))
Binciken:
A kwanakin baya ne wani dan bangare na wata gada a garin Keffi dake jihar ta Nasarawa ta ya fado tare da kashe mutane biyu.
To sai dai wannan ruftawar bangaren gadar yazo dai-dai da kaddamar da wata gada da gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya kaddamar a Birnin Lafiya a makwannin da suka gabata.
Gadar da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kaddamar gwamnan jihar yace an kashe Naira biliyan goma sha shida (N16bn) wajen gina ta.
Bincike ya tabbatar da cewa hoton dai wani bangare ne na wani bidiyo da aka samar ta amfani da kirkirarriyar basirar AI kuma aka yada a kasar India. ((https://x.com/parthadist/status/1946587824989389216?s=46)
Manhajar duba hotuna da akayi da AI mai suna Wasitai ta tabbatar da cewa hoton anyi amfani da AI ne wajen samar dashi wato dai ba na gaskiya bane.

Tuni dai aka killace wannan gada dake Keffi wacce take mallakin gwamnatin tarayya.

Sakamakon bincike: