Hukunci: Ƙarya ne
Majalisar dattawa ta bakin mai magana da yawunta ta musanta cewa majalisar ta amince da kirkirar sabbin jihohi. Sannan babu wata sahihiyar gidan jarida data rawaito ko wallafa labarin. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin an kirkiri sabbin jihohi 31 karya ne.
Shekara da shekaru dai wasu na neman a kirkiri wasu sabbin jihohi a Najeriya.
Tun bayan lokacin mulkin Soji dai ba’a kara kirkirar koda sabuwar jiha guda daya ba.
Ikirari:
Akwai dai labarin dake yaduwa matuka a shafukan sada zumunta daban-daban dake ikirarin cewa majalisun tarayya sun amince da kirkirar sabbin jihohi.
Wani shafin Facebook mai suna Abba Sani Pantami ya wallafa wannan labari inda ya sami tofa albarkacin baki wato comment sama da dubu daya da dari uku. ((https://www.facebook.com/share/p/16tDVCE6c5/?))

Haka zalika wani shafin na Facebook mai suna Nigeria Arewa shima ya wallafa wannan labari. ((https://www.facebook.com/share/p/1BzytoxNGF/?))
Wani shafin TiKTok mai suna Jabir Kaura shima yayi ikirarin amincewa da sabbin jihohi. ((https://vm.tiktok.com/ZMSnyUSxV/))
Bincike:
Binciken kafar tantance labarai ta Alkalanci ya gano cewa akwai bukatar neman kirkirar jihohi 31 dake gaban majalisun tarraya biyu.
A watan Fabrairu ne dai kwamitin yiwa kundin tsarin mulki kwaskwarima na majalisar wakilan ya gabatar da bukatar kirkirar jihohi 31.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu ya bayyana bukatar kirkirar sabbin jihohin, yayin wani zaman majalisar.
Sunayen sabbin jihohin da ake son kirkira;
Okun, Okura, da Confluence daga Kogi;
Benue Ala da Apa daga Benue;
FCT State;
Amana daga Adamawa;
Katagum daga Bauchi;
Savannah daga Borno;
Muri daga Taraba;
New Kaduna da Gurara daga Kaduna;
Tiga da Ari daga Kano;
Kainji daga Kebbi;
Etiti, Orashi, Adada, Orlu, da Aba daga kudu maso gabas.
Sauran sune Ogoja daga Cross River; Warri, Ori, and Obolo daga kudu maso kudu;
Sannan akwai Torumbe, Ibadan, Lagoon, Ijebu, da Oke Ogun/Ijesha daga kudu maso yamma.
Bayan gabatar da wannan bukata dai majalisun tarayyar biyu dole suyi zama daban-daban, da kuma jin bakin masu ruwa da tsaki kafin majalisun su amince da wannan bukata.
Mai magana da yawun majalisar dattawan Najeriya ya musanta labarin dake yaduwa cewa sun amince da kirkirar sabbin jihohi.
Babu wata sahihiyar gidan jarida daya buga ko wallafa wannan labari.
Sakamakon bincike:
Bisa musanta amincewa da kirkirar sabbin jihohi da mai magana da yawun majalisar dattawa yayi da kuma kasa samun wannan labari a kowacce sahihiyar kafar yada labarai duk da girmansa. Kafar tantance labarai ta Alkalanci bata sami wani waje da aka rawaito cewa anyi zaman amince da wannan batu ba balle batun zaman masu ruwa da tsaki. Wadannan dalilai na rashin ingantattun bayanai yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa labarin dake yaduwa kan an kirkiri sabbin jihohi karya ne.
