BindiddigiKarya ne: Kashin Bera baya maganin appendix

Karya ne: Kashin Bera baya maganin appendix

-

Hukunci: Ƙarya ne
Bisa bayanan hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO, hukumar kare yaduwar cututtuka da ma sauran hukumomin lafiya na duniya da suka bayyana cewa kashin Bera na haddasa cututtuka iri-iri misali zazzabin Lassa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin kashin Bera na maganin Appendix karya ne
Ikirari:
Akwai wani bidiyo mai tsawon sakan arba’in dake yaduwa a kafar sada zumunta ta Facebook da aka ji wani na ikirari cewa  kashin bera yana maganin appendix.
Ana samun kashin Bera a tara su da yawa, Idan aka tara sai a jika su a cikin ruwa, Idan aka jika ya jiku sai a rika bawa mai wannan shiwon yana sha. In dai yana sha Allah zai umarci wadannan tsakuwowin dake jikin sa su narke…)
Wannan bidiyo dai ya sami wadanda suka kalla sama da dubu ashirin.
Bincike:
Bera dai na cikin dabbobin da hukumomin lafiya suka sanya a matsayin mai yada cutuka zuwa ga mutum.
Hukumar lafiya ta duniya wato WHO tace kashi 60% na cututtuka masu yaduwa da aka fitar da bullar su a fadin duniya ana samunsu ne daga dabbobi. Haka zalika hukumar ta ce cututtukan da ake samu daga dabbobi na sanadiyyar mutuwar mutane miliyoyi kowacce shekara a fadin duniya.
Hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO ta bayyana cewa Bera na yada cutar zazzabin Lassa zuwa ga mutane, da zarar abincin da mutane suka ci ya gauraya da fitsari ko kashin Beran da ke dauke da kwayar cutar. Shi wannan Beran dai hukumar ta ce ana samun sa sosai a wasu kasashen yammacin Afrika wato harda Najeriya.
Zazzabin Lassa a Najeriya
Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce akalla mutane sama da dari biyu ne suka mutu sanadiyyar cutar zazzabin Lassa a shekarar 2024.
Hoton rahoton hukumar NCDC kan zazzabin Lassa
Hukumar ta gargadi mutane da su guji cin Bera ko kuma barin kayayyakin abinci a bude inda Bera ka iya yin kashi ko fitsari a ciki.
Kungiyar bada tallafin magungunan riga kafi ta Gavi ta ce akalla mutane miliyan biyu da dubu dari bakwai ne ke kamuwa da zazzabin Lassa a duk shekara.
Masu bincike kan harkar lafiya sun bayyana cewa kashin Bera na da matukar hadari domin yana iya yada cututtuka sosai, musamman masu yaduwa wanda ka iya haddasa asarar rayuka.
Babu dai inda a kimiyyance aka ce kashin Bera na da wani magani fyace cutarwa.
Sakamakon Bincike:
Bisa bayanan hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya WHO, hukumar kare yaduwar cututtuka da ma sauran hukumomin lafiya na duniya da suka bayyana cewa kashin Bera na haddasa cututtuka iri-iri misali zazzabin Lassa. Wannan yasa Alkalanci yanke hukuncin cewa ikirarin kashin Bera na maganin Appendix karya ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sababbin Labarai

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta ta TikTok wanda ke nuna cewa jami'an tsaro sun kwashe...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON wanda Najeriya ta zo ta biyu, akwai labarai kala-kala...

Bidiyon da ake yaɗawa ba na waɗanda sukai kisan Ɗorayi bane 

Ƴan Najeriya dai na cigaba da jimami tare da Allah wadai da kisan wasu ƴan gida ɗaya su bakwai...

Hotunan samuwar makaman kariya zuwa Burkina Faso daga Rasha da China hadin AI ne

  Yayin da Rasha da ƙasar Sin ke ci gaba da tura makamai zuwa yankin Sahel, wani hoto da bidiyo...

Labarin cewa Aisha Buhari ta amince ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ne

Tun bayan kammala iddar tsohuwar matar shugaban kasa Muhammadu Buhari ake ta yada wasu labarai da iƙirarai kala-kala wanda...

Gwamna Abba Kabir Yusuf bai cire Mustapha Kwankwaso daga muƙaminsa ba

A ƙarshen watan Disemba ne dadi aka sami labarin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa...

Karanta wannan

Ina gaskiyar Iƙirarin mai da waɗanda ake zargi da kisa a Kano zuwa kudancin Najeriya?

IƙirariWani bidiyo yana ta yaɗuwa a kafar sada zumunta...

Ina gaskiyar labari da hotunan baiwa ƴan wasan Super Eagles gidaje da motoci

Bayan da aka kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka...

Kuna iya kuma soDANGANTAKA
An ba ku shawarar